Publicidade

Salmos 140

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.

1 Ka cece ni, ya Ubangiji, daga mugaye;

ka tsare ni daga mutane masu rikici,

2 masu shirya maƙarƙashiya a zukatansu

suna kuma kawo yaƙi kullum.

3 Suna sa harsunansu su yi kaifi kamar na maciji;

dafin gamsheƙa yana a leɓunansu. Sela

4 Ka kiyaye ni, ya Ubangiji, daga hannuwan mugaye;

ka tsare ni daga mutane masu rikici

waɗanda suke shirin kwashe ni a ƙafafu.

5 Masu girman kai sun sa mini tarko;

sun shimfiɗa igiyoyin ragarsu

sun kuma shirya mini tarko a hanyata. Sela

6 Ya Ubangiji, na ce maka, "Kai ne Allahna."

Ka ji kukata ta neman jinƙai, ya Ubangiji.

7 Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mai fansana mai ƙarfi,

wanda yake garkuwoyin kaina a ranar yaƙi.

8 Kada ka biya wa mugaye bukatunsu, ya Ubangiji;

kada ka bar shirinsu su yi nasara,

in ba haka ba za su yi fariya. Sela

9 Bari kawunan waɗanda suka kewaye ni

su rufu da masifun da leɓunansu suka jawo.

10 Bari garwashin wuta yă zubo a kansu;

bari a jefar da su cikin wuta,

cikin rami mai zurfi, kada su sāke tashi.

11 Kada masu ɓata suna su taɓa kahu a ƙasar;

bari masifa ta farauci mutane masu rikici.

12 Na san cewa Ubangiji ya shirya wa matalauta adalci

yana kuma yi wa mabukata adalci.

13 Tabbatacce masu adalci za su yabi sunanka

masu aikata gaskiya kuma za su zauna a gabanka.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_06-50-08-