Publicidade

Salmos 46

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce.

1 Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,

kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.

2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza

duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,

3 ko da ruwansa suna ruri suna kumfa

duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Sela

4 Akwai kogi mai rafuffukan da suke sa birnin Allah murna,

tsattsarkan wuri inda Mafi Ɗaukaka ke zama.

5 Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba;

Allah zai taimake ta da safe.

6 Al’ummai suna hayaniya, mulkoki sun fāɗi;

ya ɗaga muryarsa, duniya ta narke.

7 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu;

Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela

8 Zo ku ga ayyukan Ubangiji,

kangon da ya kawo a kan duniya.

9 Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit

ko’ina a duniya.

Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu,

ya ƙone garkuwoyi da wuta.

10 "Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah;

za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai,

za a ɗaukaka ni cikin duniya."

11 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu;

Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_06-50-08-