Pular para o conteúdo
Publicidade

Zabura 137

1 A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kuka

sa’ad da muka tuna da Sihiyona.

2 A can a kan rassan itatuwa

muka rataye garayunmu,

3 gama a can masu kamunmu suka sa mu yi waƙoƙi,

masu ba mu azaba suka nema waƙoƙin farin ciki;

suka ce, "Ku rera mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona!"

4 Yaya za mu rera waƙoƙin Ubangiji

a baƙuwar ƙasa?

5 In na manta da ke, ya Urushalima,

bari hannuna na dama manta da iyawarsa.

6 Bari harshena manne wa rufin bakina

in ban tuna da ke ba,

in ban so Urushalima

farin cikin mafi girma ba.

7 Ka tuna, ya Ubangiji, abin da mutanen Edom suka yi

a ranar da Urushalima ta fāɗi.

Suka yi ihu suka ce, "A ragargaza ta,

A ragargaza ta har tushenta!"

8 Ya Diyar Babilon, an ƙaddara ke zuwa hallaka,

mai farin ciki ne wanda ya sāka miki

saboda abin da kika yi mana,

9 shi da ya ƙwace jariranki

ya fyaɗa su a kan duwatsu.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também