Pular para o conteúdo
Publicidade

Zabura 93

1 Ubangiji yana mulki, yana sanye da ɗaukaka;

Ubangiji yana sanye da ɗaukaka yana kuma sanye da ƙarfi.

An kafa duniya daram; ba za a iya matsar da ita ba.

2 An kafa kursiyin tun da daɗewa;

kana nan tun fil azal.

3 Tekuna sun taso, ya Ubangiji,

tekuna sun ta da muryarsu;

tekuna sun da ta raƙumansu masu tumbatsa.

4 Mafi ƙarfi fiye da tsawan manyan ruwaye,

mafi ƙarfi fiye da ikon raƙuman ruwan teku,

Ubangiji mai zama a bisa mai girma ne.

5 Ƙa’idodinka suna nan daram;

tsarki ya yi wa gidanka ado

har kwanaki marar ƙarewa, ya Ubangiji.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também