Publicidade

Salmos 127

Waƙar haurawa. Ta Solomon.

1 In ba Ubangiji ne ya gina gida ba,

masu gininta suna wahala a banza ne.

In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba,

masu tsaro suna yin tsaro a banza.

2 Banza ne ka farka da wuri

ka koma da latti,

kana fama don abincin da za ka ci,

gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna.

3 ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,

yara lada ne daga gare shi.

4 Kamar kibiyoyi a hannun jarumi

haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.

5 Mai albarka ne mutumin

da korinsa sun cika da su.

Ba za a kunyata su ba

sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_14-04-22-