Publicidade

Salmos 21

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.

1 Ya Ubangiji, sarki yana farin ciki cikin ƙarfinka.

Yana farin cikinsa ƙwarai cikin nasarorin da ka ba shi!

2 Ka biya masa bukatar zuciyarsa

ba ka kuwa hana masa roƙon da ya yi da leɓunansa ba. Sela

3 Ka marabce shi da yalwar albarka

ka kuma sa masa rawanin zallan zinariya a kansa.

4 Ya nemi ka ba shi rai, ka kuwa ba shi,

tsawo kwanaki, har abada abadin

5 Ta wurin nasarorin da ka ba shi, ɗaukakarsa mai girma ce;

ka mayar masa ɗaukaka da kuma suna.

6 Tabbatacce ka ba shi madawwamiyar albarka

ka kuma sa shi murna da farin cikin kasancewarka.

7 Gama sarki ya dogara gare ka Ubangiji

ta wurin ƙauna marar ƙarewa ta Mafi Ɗaukaka

ba zai jijjigu ba.

8 Hannunka zai kakkama dukan abokan gābanka;

hannunka na dama zai kakkama masu ƙinka.

9 A lokacin bayyanarka

za ka sa su zama kamar wutar matoya.

Cikin fushinsa Ubangiji zai haɗiye su,

kuma wutarsa za tă cinye su.

10 Za ka hallaka ’ya’yansu daga duniya,

zuriyarsu kuma daga ’yan adam.

11 Ko da yake suna shirya maka mugunta

suna kuma ƙirƙiro mugayen dabaru, ba za su yi nasara ba;

12 gama za ka sa su juye bayansu

sa’ad da ka auna su da bakan da ka ja.

13 Ka sami ɗaukaka, ya Ubangiji cikin ƙarfinka;

za mu rera mu kuma yabi ikonka.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_06-50-08-