Pular para o conteúdo
Publicidade

Zabura 53

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat.53.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. Wani maskil53.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. na Dawuda.

1 Wawa ne kawai yakan ce a zuciyarsa,

"Ba Allah."

Sun lalace, kuma hanyoyinsu ba su da kyau;

babu wani mai aikata abu mai kyau.

2 Allah yana duba daga sama

a kan ya’yan mutane

ga ko akwai wani wanda ya gane,

wani wanda yake neman Allah.

3 Kowa ya kauce, gaba ɗaya sun lalace;

babu guda da yake aikata abu mai kyau,

babu ko ɗaya.

4 Masu aikata mugunta ba sa taɓa koyo?

Suna cin mutanena kamar yadda ake cin burodi,

ba sa kuma kira ga Allah.

5 Ga shi fa, sun firgita don tsoro,

ko da yake babu dalilin tsoro,

gama Allah zai watsar da ƙasusuwan masu ƙinsa,

za su sha kunya, gama Allah ya ƙi su.

6 Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana!

Sa’ad da Allah ya sāke arzuta mutanensa,

bari Yaƙub yi farin ciki Isra’ila kuma yi murna!

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também