Publicidade

Salmos 75

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Mai muryar "Kada A Hallaka." Zabura ta Asaf. Waƙa ce.

1 Muna maka godiya, ya Allah,

muna maka godiya, gama Sunanka yana kusa;

mutane na faɗin ayyukanka masu banmamaki.

2 Ka ce, "Na zaɓi ƙayyadadden lokaci;

ni ne wanda yake shari’ar gaskiya.

3 Sa’ad da duniya da dukan mutanenta suka girgiza,

ni ne wanda na riƙe ginshiƙan daram. Sela

4 Ga masu girman kai na ce, ‘Kada ku ƙara taƙama,’

ga mugaye kuma, ‘Kada ku ɗaga ƙahoninku.

5 Kada ku ɗaga ƙahoninku gāba da sama;

kada ku yi magana da miƙaƙƙen wuya.’ "

6 Ba wani daga gabas ko yamma

ko hamada da zai ɗaukaka mutum.

7 Amma Allah ne mai yin shari’a,

yakan saukar da wannan, yă kuma tayar da wani.

8 A hannun Ubangiji akwai kwaf

cike da ruwan inabi mai kumfa gauraye da kayan yaji;

yakan zuba shi, dukan mugayen duniya kuwa

su sha shi tas.

9 Game da ni dai, zan furta wannan har abada;

zan rera yabo ga Allah na Yaƙub,

10 wanda ya ce, "Zan yanke ƙahonin dukan mugaye,

amma za a ɗaga ƙahonin adalai sama."

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_06-50-08-