Publicidade

Salmos 20

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda.

1 Ubangiji ya amsa maka sa’ad da ka yi kira cikin wahala;

bari sunan Allah na Yaƙub yă kiyaye ka.

2 Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarki

yă kuma ba ka gudummawa daga Sihiyona.

3 Bari yă tuna da dukan sadakokinka

yă kuma karɓi hadayunka na ƙonawa. Sela

4 Bari yă biya maka bukatan ranka

yă kuma sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.

5 Za mu yi sowa ta farin ciki sa’ad da ka yi nasara

mu kuma ɗaga tutotinmu a cikin sunan Allahnmu.

Bari Ubangiji yă biya maka dukan bukatunka.

6 Yanzu na san cewa,

Ubangiji yakan cece shafaffensa.

Yakan amsa masa daga samansa mai tsarki

da ikon ceto na hannun damansa.

7 Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai,

amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu.

8 Za a durƙusar da su, su kuma fāɗi,

amma mu za mu tashi mu tsaya daram.

9 Ya Ubangiji, ka ba da nasara ga sarki!

Ka amsa mana sa’ad da muka yi kira!

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_18-40-07-