Pular para o conteúdo
Publicidade

Zabura 123

Waƙar haurawa.

1 Na da idanuna gare ka,

gare ka da kursiyinka yake cikin sama.

2 Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu,

kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta,

haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu,

sai ya nuna mana jinƙansa.

3 Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai,

gama mun jimre da reni mai yawa.

4 Mun jimre da wulaƙanci

daga masu girman kai,

reni mai yawa daga masu fariya.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também