Publicidade

Salmos 57

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar "Kada Ka Hallaka." Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da ya gudu daga Shawulu zuwa cikin kogo.

1 Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai,

gama a gare ka raina yake samun mafaka.

Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka

sai masifar ta wuce.

2 Na yi kuka ga Allah Mafi Ɗaukaka,

ga Allah, wanda yake cika manufarsa gare ni.

3 Ya aika daga sama ya kuwa cece ni,

yana tsawata wa waɗanda suke fafarata da zafi; Sela

Allah yakan aika da ƙaunarsa da amincinsa.

4 Ina tsakiyar zakoki;

ina kwance a cikin namun jeji masu cin mutane,

mutanen da haƙoransu masu ne da kuma kibiyoyi,

waɗanda harshensu suna da kaifi kamar takobi.

5 Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai;

bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.

6 Sun shimfiɗa raga don su kama ƙafafuna,

damuwa ta sha ƙarfina.

Sun haƙa rami a hanyata,

amma su kansu suka fāɗa a cikinta. Sela

7 Zuciyata tana nan daram, ya Allah,

zuciyata tana nan daram;

zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe.

8 Ka farka, raina!

Ku farka, garaya da molo!

Zan sa safe yă farka.

9 Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai;

zan rera game da kai a cikin mutane.

10 Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai;

amincinka na kaiwa sarari.

11 Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai;

bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_06-50-08-