Publicidade

Salmos 100

Zabura ce. Don yin godiya.

1 Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya.

2 Yi wa Ubangiji sujada da murna;

ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki.

3 Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah.

Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne;

mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa.

4 Ku shiga ƙofofinsa da godiya

filayen gidansa kuma da yabo;

ku gode masa ku kuma yabi sunansa.

5 Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada;

amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_18-40-07-