Publicidade

Salmos 122

Waƙar haurawa. Ta Dawuda.

1 Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni,

"Bari mu tafi gidan Ubangiji."

2 Ƙafafunmu suna tsaye

a ƙofofinki, ya Urushalima.

3 An gina Urushalima kamar birnin

da aka yi a harhaɗe wuri guda.

4 A can ne kabilu suke haurawa,

kabilan Ubangiji,

don su yabi sunan Ubangiji

bisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila.

5 A can kursiyoyin shari’a yake tsaye,

kursiyoyin gidan Dawuda.

6 Ku yi addu’a don salamar Urushalima,

"Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya.

7 Bari salama ta kasance a katangarki

zaman lafiya kuma a fadodinki."

8 Saboda ’yan’uwana da kuma abokaina,

zan ce, "Salama tă kasance tare da ke."

9 Saboda gidan Ubangiji Allahnmu,

zan nemi wadatarki.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_14-04-22-