Publicidade

Salmos 120

Waƙar haurawa.

1 Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata,

ya kuwa amsa mini.

2 Ka cece ni, ya Ubangiji,

daga leɓuna masu ƙarya

da kuma daga harsuna masu yaudara.

3 Me zai yi maka,

me kuma ya fi,

ya kai harshe mai yaudara?

4 Zai hukunta ku da kibiyoyi masu tsini na jarumi,

tare da garwashin wuta na itacen tsintsiya.

5 Kaitona da nake zama a Meshek,

da nake zama a ciki tentunan Kedar!

6 Da daɗewa na zauna

a cikin waɗanda suke ƙin salama.

7 Ni mutum ne mai salama;

amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_14-04-22-