Publicidade

Salmos 52

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Wani maskil ta Dawuda. Sa’ad da Doyeg mutumin Edom ya tafi wurin Shawulu ya ce masa, "Dawuda ya tafi gidan Ahimelek."

1 Me ya sa kake fariya game da mugunta, kai babban mutum?

Me ya sa kake fariya dukan yini,

kai da kake abin kunya a idanun Allah?

2 Harshenka kan shirya hallaka;

yana nan kamar reza mai ci,

kana ta ruɗu.

3 Kana ƙaunar mugunta fiye da alheri,

ƙarya a maimakon faɗin gaskiya. Sela

4 Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa,

Ya kai harshe mai ruɗu!

5 Tabbatacce Allah zai kai ka ga madawwamiyar hallaka.

Zai fizge ka yă yayyage ka daga tentinka;

zai tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. Sela

6 Masu adalci za su ga su ji tsoro;

za su yi masa dariya, suna cewa,

7 "Yanzu, ga mutumin

da bai mai da Allah mafakarsa ba

amma ya dogara a yawan arzikinsa

ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!"

8 Amma ni kamar itace zaitun ne

ina haɓaka a gidan Allah;

na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allah

har abada abadin.

9 Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi;

a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau.

Zan yabe ka a gaban tsarkakanka.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_18-40-07-