Publicidade

Salmos 12

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi. Bisa ga sheminit. Zabura ta Dawuda.

1 Ka taimaka, Ubangiji, gama masu tsoron Allah ba sa nan kuma;

masu aminci sun ɓace daga cikin mutane.

2 Kowa yana yi wa maƙwabcinsa ƙarya;

zaƙin bakinsu maganar ƙarya ce

suna cike da ruɗu a zukatansu.

3 Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu

da kuma kowane harshe mai fariya,

4 masu cewa,

"Da harsunanmu za mu yi nasara;

leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?"

5 "Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata,

zan tashi yanzu," in ji Ubangiji.

"Zan kāre su daga masu yin musu sharri."

6 Kalmomin Ubangiji kuwa ba su da kuskure,

kamar azurfan da aka tace cikin matoyan yumɓu,

aka tsabtacce sau bakwai.

7 Ya Ubangiji, za ka kiyaye mu lafiya

ka tsare mu daga irin mutanen nan har abada.

8 Mugaye suna yawo a sake

sa’ad da ake girmama abin da ba shi da kyau a cikin mutane.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_09-43-29-