Publicidade

Salmos 128

Waƙar haurawa.

1 Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji,

waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.

2 Za ka ci amfanin aikinka;

albarku da wadata za su zama naka.

3 Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya

a cikin gidanka;

’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun

kewaye da teburinka.

4 Ta haka mai albarka yake

wanda yake tsoron Ubangiji.

5 Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona

dukan kwanakin ranka;

bari ka ga wadatar Urushalima,

6 bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka.

Salama tă kasance tare da Isra’ila.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_14-04-22-