Publicidade

Salmos 82

Zabura ta Asaf.

1 Allah yana shugabanta cikin babban taro;

yakan zartar da hukunci a cikin "alloli".

2 "Har yaushe za ku kāre marasa adalci

ku kuma goyi bayan mugaye? Sela

3 Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu;

ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.

4 Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata;

ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.

5 "Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba.

Suna yawo cikin duhu;

an girgiza dukan tussan duniya.

6 "Na ce, ‘Ku "alloli" ne;

dukanku ’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne.

7 Amma za ku mutu kamar mutum kurum;

za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki."

8 Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya,

gama dukan al’ummai gādonka ne.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-18_10-32-54-