Publicidade

Salmos 3

Zabura ta Dawuda. Sa’ad da ya gudu daga ɗansa Absalom.

1 Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne!

Su nawa suke gāba da ni!

2 Da yawa suna magana a kaina suna cewa,

"Allah ba zai cece shi ba." Sela

3 Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji;

ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.

4 Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi,

ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela

5 Na kwanta na yi barci;

na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.

6 Ba zan ji tsoro ko dubu goma

suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.

7 Ka tashi Ya Ubangiji!

Ka cece ni, ya Allahna!

Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi;

ka kakkarya haƙoran mugaye.

8 Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo.

Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Sela

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-15_21-32-39-