Publicidade

Salmos 32

Ta Dawuda. Maskil ne.

1 Mai farin ciki ne shi

wanda aka gafarta masa laifofinsa,

wanda aka shafe zunubansa.

2 Mai farin ciki ne mutumin

da Ubangiji ba ya lissafin zunubinsa a kansa

wanda kuma babu ruɗu a ruhunsa.

3 Sa’ad da na yi shiru,

ƙasusuwana sun yi ta mutuwa

cikin nishina dukan yini.

4 Gama dare da rana

hannunka yana da nauyi a kaina;

an shanye ƙarfina ƙaf

sai ka ce a zafin bazara. Sela

5 Sa’an nan na furta zunubina a gare ka

ban kuwa ɓoye laifina ba.

Na ce, "Zan furta

laifofina ga Ubangiji."

Ka kuwa gafarta

laifin zunubina. Sela

6 Saboda haka bari duk mai tsoron Allah yă yi addu’a gare ka

yayinda kake samuwa;

tabbatacce sa’ad da manyan ruwaye suka taso,

ba za su kai wurinsa ba.

7 Kai ne wurin ɓuyata;

za ka tsare ni daga wahala

ka kewaye ni da waƙoƙin ceto. Sela

8 Zan umarce ka in kuma koyar da kai a hanyar da za ka bi;

Zan ba ka shawara in kuma lura da kai.

9 Kada ka zama kamar doki ko doki,

wanda ba su da azanci

wanda dole sai an bi da su da linzami da ragama

in ba haka ba, ba za su zo wurinka ba.

10 Azaban mugu da yawa suke,

amma ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa

kan kewaye mutumin da ya dogara gare shi.

11 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji ku kuma yi murna, ku adalai;

ku rera, dukanku waɗanda zuciyarku take daidai!

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_18-40-07-