Publicidade

Salmos 43

1 Ka nuna ni marar laifi ne, ya Allah,

ka kuma nemi hakkina

a kan al’ummai marasa sanin Allah.

Ka kuɓutar da ni daga

masu ruɗu da mugayen mutane.

2 Kai ne Allah mafakata.

Me ya sa ka ƙi ni?

Me zai sa in yi ta yawo ina makoki,

a danne a hannun abokin gāba?

3 Ka aiko da haskenka da gaskiyarka,

bari su bishe ni

bari su kawo ni ga dutsenka mai tsarki,

zuwa wurin da kake zama.

4 Sa’an nan zan tafi bagaden Allah,

ga Allah, farin cikina da murnata.

Zan yabe ka da garaya,

Ya Allah, Allahna.

5 Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina?

Me ya sa ka damu a cikina?

Ka dogara ga Allah,

gama zai sāke yabe shi,

Mai Cetona da Allahna.

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-16_18-40-07-