Publicidade

Coração quebrantado

Por Bíblia Online

Deus está perto dos que têm o coração quebrantado. A Bíblia consola os aflitos: o sacrifício que Deus aceita é o espírito quebrantado e um coração contrito — jamais desprezará.

Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai

ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.

Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu;

karyayyiya da kuma zuciya mai tuba,

Ya Allah, ba za ka ƙi ba.

Ya warkar da masu raunanar zuciya

ya ɗaɗɗaura miyakunsu.

Jikina da zuciyata za su iya raunana,

amma Allah ne ƙarfin zuciyata

da kuma rabona har abada.

Gama abin da Maɗaukaki da kuma Mai daraja ya faɗa

wanda yake raye har abada, wanda sunansa mai tsarki ne,

"Ina zama a bisa da kuma a tsattsarkan wuri,

amma kuma tare da shi wanda yake mai halin tuba mai tawali’u a ruhu,

don in farfaɗo da ruhu mai tawali’u

in kuma farfaɗo da zuciyar mai halin tuba.

Ba hannuna ba ne ya yi dukan waɗannan abubuwa,

ta haka suka kasance?"

In ji Ubangiji.

"Wannan mutum ne nake jin daɗi,

shi da yake mai ƙasƙanci da kuma zuciyar yin tuba,

yana kuma rawar jiki ga maganata.

Shekarar tagomashin Ubangiji

Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina,

domin Ubangiji ya shafe ni

domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta.

Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci,

don in yi shelar yanci don ɗaurarru

in kuma kunce yan kurkuku daga duhu

don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji

da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu,

don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki,

in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona,

in maido musu rawani mai kyau

a maimako na toka,

man murna

a maimako na makoki,

da kuma rigar yabo

a maimako na ruhun fid da zuciya.

Za a ce da su itatuwan oak na adalci,

shukin Ubangiji

don bayyana darajarsa.

"Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu,

gama mulkin sama nasu ne.

Masu albarka ne waɗanda suke makoki,

gama za a yi musu ta’aziyya.

Masu albarka ne waɗanda suke masu tawali’u,

gama za su gāji duniya.

Baƙin ciki irin na tsoron Allah yana kai ga tuban da yake kawo ceto, ba ya kuma kawo baƙin ciki, amma baƙin ciki irin na duniya yakan kawo mutuwa. Ku dubi abin da wannan baƙin ciki irin na tsoron Allah ya kawo muku mana, ya sa ku marmarin aikatawa, da nuna cewa kun yi kuskure, ya sa kuka yi fushi, kuka kuma ji tsoro, ya sa kuka sa zuciya, kuka kuma sa aniya, ya sa kuna a shirye ku ga an yi horon da ya dace. Game da wannan sha’ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi.

Amma ya ce mini, "Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona." Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi zauna tare da ni.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-