Corpo é o templo de Deus
O corpo do cristão é templo de Deus. Ele habita em nós pelo Espírito Santo, fazendo do crente morada viva e sagrada do Altíssimo.
Templo do Deus vivo
Vós sois o templo do Deus vivo. Deus disse: habitarei neles e entre eles andarei. O criador mora em sua criação redimida.
Ashe, ba ku sani ba cewa ku kanku haikalin Allah ne, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikinku? Duk wanda ya ɓata haikalin Allah, Allah zai ɓata shi, don haikalin Allah mai tsarki ne, ku ne kuwa haikalin nan.
Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne; saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.
Wane alkawari ne tsakanin haikalin Allah da na gumaka? Gama mu haikalin Allah mai rai ne. Kamar yadda Allah ya ce,
"Zan zauna tare da su,
in yi tafiya a cikinsu,
zan zama Allahnsu,
su kuma za su zama mutanena."
Don haka, yanzu ku ba baƙi ba ne, ku kuma ba bare ba ne. Ku ’yan ƙasa ne tare da mutanen Allah, iyalin gidan Allah kuma. Ku gini ne wanda manzanni da annabawa suke tushensa, Kiristi kuma shi ne dutse mafi muhimmanci na ginin. Ta wurinsa ne dukan ginin yake a haɗe, shi ne kuma yake sa ginin yă yi girma, yă zama haikali mai tsarki domin Ubangiji. Ku ma sashe ne na wannan ginin da Kiristi ya yi inda Allah yake zaune ta wurin Ruhunsa.
Gama kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma maginin dukan abu Allah ne. Musa ya yi aminci a matsayin bawa cikin dukan gidan Allah, yana ba da shaida a kan abubuwan da za a faɗa nan gaba. Amma Kiristi mai aminci ne kamar ɗa a gidan Allah. Mu kuwa gidansa ne, in muka tsaya gabanmu gadi da kuma begen da muke taƙama a kai.
Musa ya yi aminci a matsayin bawa cikin dukan gidan Allah, yana ba da shaida a kan abubuwan da za a faɗa nan gaba. Amma Kiristi mai aminci ne kamar ɗa a gidan Allah. Mu kuwa gidansa ne, in muka tsaya gabanmu gadi da kuma begen da muke taƙama a kai.
Cristo em nós
Já não sou eu quem vive, mas Cristo vive em mim. A presença de Deus no crente é privilégio e responsabilidade sagrada.
An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.
Yesu ya amsa ya ce, "Duk mai ƙaunata, zai yi biyayya da koyarwata. Ubana zai ƙaunace shi, za mu kuwa zo wurinsa mu zauna tare da shi.
Kira don a adana bangaskiya
Saboda haka, ’yan’uwa, da yake muna da wannan tabbaci na shiga Wuri Mafi Tsarki ta wurin jinin Yesu, ta wurin sabuwa, rayayyiyar hanya kuma wadda aka buɗe mana ta labulen nan, wato, jikinsa, da yake kuma muna da babban firist mai mulkin gidan Allah, bari mu matso kusa da Allah da zuciya mai gaskiya da kuma cikakken tabbaci mai zuwa ta wurin bangaskiya. Bari mu bar zukatan da tsabta, lamirinmu babu mugunta, da kuma jikunanmu a wanke da ruwa.
Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.