Tomar uma decisão
Tomar decisões com sabedoria é um dos maiores desafios da vida. A Bíblia nos ensina a buscar a Deus em oração, na Palavra e no conselho, confiando que Ele dirige os nossos passos.
Buscar a Deus
Se algum de vós tem falta de sabedoria, peça a Deus. Ele dá generosamente e sem repreensão a todos os que pedem.
In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.
Wannan shi ne ƙarfin halin da muke da shi sa’ad da muke zuwa a gaban Allah, gama mun san cewa kome muka roƙa bisa ga nufinsa, yakan saurare mu.
In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.
Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka
kada kuma ka dangana ga ganewarka;
cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,
zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,
zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
Gama na san shirye-shiryen da na yi muku," in ji Ubangiji, "shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.
Conselho e direção
Onde não há conselho os planos se frustam. Toda Escritura é útil para nos guiar nas decisões da vida.
Saboda rashin jagora al’umma takan fāɗi,
amma masu ba da shawara da yawa kan tabbatar da nasara.
Akan jefa ƙuri’a a kan cinya,
amma kowace shawara mai kyau daga Ubangiji ne.
Mutumin da ba ya abokantaka yakan nema ya cika burinsa ne kaɗai;
yakan ƙi yarda da kowace maganar da take daidai.
Wawa ba ya sha’awa ya sami fahimta
amma abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya ba da ra’ayinsa.
Sa’ad da mugunci ya zo, reni ma kan zo,
haka kuma sa’ad da kunya ta zo, shan kunya kan biyo.
Kalmomin bakin mutum suna da zurfi kamar ruwaye,
amma maɓulɓulan hikima rafi ne mai gudu.
Ba shi da kyau ka yi wa mugu alheri
ko ka hana wa marar laifi adalci.
Leɓunan wawa kan jawo masa faɗa,
bakinsa kuma kan gayyaci dūka.
Bakin wawa lalatar da kansa yake yi
leɓunansa kuma tarko ne ga ransa.
Kalmomin mai gulma kamar abinci mai daɗi suke;
sukan gangara zuwa can cikin gaɓoɓin mutum.
Wanda yake ragwanci a aikinsa
ɗan’uwa ne ga wanda yakan lalatar da abubuwa.
Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi;
masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya.
Dukiyar masu arziki ita ce birninsu mai katanga;
suna gani cewa ba za a iya huda katangar ba.
Kafin fāɗuwarsa zuciyar mutum takan yi girman kai,
amma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.
Duk wanda yakan ba da amsa kafin ya saurara,
wannan wauta ce da kuma abin kunya.
Sa rai da mutum ke yi kan taimake shi sa’ad da yake ciwo,
amma in ya karai, to, tasa ta ƙare.
Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci,
domin mutumin Allah yă zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.
Da suka isa kan iyakar Misiya, suka yi ƙoƙari su shiga Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai yarda musu ba.
A ikkilisiyar da take a Antiyok akwai waɗansu annabawa da malamai. Barnabas, Siman wanda ake kira Baƙi, Lusiyus mutumin Sairin, Manayen (wanda aka goya tare da Hiridus mai mulki), da kuma Shawulu. Yayinda suna cikin sujada da azumi ga Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki ya ce, "Ku keɓe mini Barnabas da Shawulu domin aikin da na kira su." Saboda haka bayan suka yi azumi da addu’a, sai suka ɗibiya musu hannuwansu a kansu suka sallame su.
Confiar e seguir
Seja o que for que façais, fazei tudo para a glória de Deus. O sábio ouve a Deus antes de agir.
Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah.
Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa.
A Gibeyon, Ubangiji ya bayyana ga Solomon da dare a mafarki, Allah ya ce, "Ka roƙi abin da kake so in ba ka."
Solomon ya amsa ya ce, "Ka nuna alheri mai girma ga bawanka, mahaifina Dawuda domin ya yi aminci gare ka da adalci, ya kuma kasance da zuciya mai gaskiya. Ka ci gaba da wannan alheri mai girma gare shi, ka ba shi ɗa don yă zauna a kujerar sarautarsa a wannan rana.
"Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka sa bawanka a wurin mahaifina Dawuda. Amma ni ɗan yaro ne kawai, ban kuma san yadda zan yi ayyukana ba. Bawanka yana nan a cikin mutanen da ka zaɓa, mutane masu girma, waɗanda suka wuce ƙirge, ko a lissafta. Saboda haka ka ba bawanka zuciyar ganewa, don yă shugabanci mutanenka, yă kuma iya rarrabe tsakanin abin da yake daidai da abin da ba daidai ba. Gama wa zai iya shugabance wannan mutanenka masu girma haka?"
Sai Ubangiji ya ji daɗi cewa Solomon ya roƙa wannan. Saboda haka Allah ya ce masa, "Da yake ka nemi wannan ne, ba ka kuwa nemi tsawon rai ko arziki wa kanka ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, amma ka nemi ganewa a aikata gaskiya, zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har yă zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba.
Matarsa ta ce masa, "Har yanzu kana nan da amincinka? Ka la’anta Allah ka mutu!"
Ya amsa ya ce, "Kina magana kamar wawiya. Alheri kaɗai za mu dinga samu daga Allah ban da wahala?"
A cikin wannan duka Ayuba bai yi zunubi ba cikin maganarsa.