Pular para o conteúdo
Publicidade

Deus está contigo

Por Bíblia Online

Deus está contigo — esta é a promessa mais repetida da Bíblia. Onde quer que vás, em qualquer situação, o Senhor caminha ao teu lado e nada pode te separar do seu amor.

Eu sou contigo

Sê forte e corajoso! Não temas, porque o Senhor teu Deus é contigo por onde quer que andares.

Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je."

Ba wanda zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai; ba zan taɓa rabuwa da kai ba; ba zan yashe ka ba.

"Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, gama kai za ka bi da mutanen nan har su karɓi ƙasar da na yi wa kakanninsu alkawari zan ba su.

Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yashe ku ba."

Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai;

kada ka karai, gama ni ne Allahnka.

Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka;

zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.

Zan mai da kai katanga ga wannan mutane,

katanga mai ƙarfi na tagulla;

za su yi yaƙi da kai

amma ba za su yi nasara a kanka ba,

gama ina tare da kai

don in kuɓutar in kuma cece ka,"

in ji Ubangiji.

Sa’ad da mala’ikan Ubangiji ya bayyana wa Gideyon, sai ya ce masa, "Ubangiji yana tare da kai, jarumi."

Presença constante

Não te deixarei nem te desampararei. Cristo habita no coração pela fé — e estará conosco até o fim dos tempos.

Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,

"Ba zan taɓa bar ka ba;

ba zan taɓa yashe ka ba."

kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani."

Ina addu’a domin Kiristi zauna a cikin zukatanku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu’a saboda ku da kuka kahu sosai cikin ƙauna,

Ashe, ba ku sani ba cewa ku kanku haikalin Allah ne, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikinku?

Ga ni! Ina tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa. Duk wanda ya ji muryata ya kuma buɗe ƙofar, zan shiga in kuma ci tare da shi, shi kuma tare da ni.

Amor inseparável

Nada poderá nos separar do amor de Deus que está em Cristo Jesus nosso Senhor. Absolutamente nada.

Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

Seja o primeiro