Dinheiro
O dinheiro é ferramenta que pode ser usada para o bem ou para o mal. A Bíblia nos ensina a administrar recursos com sabedoria, generosidade e temor ao Senhor.
Perspectiva bíblica
Guardai-vos da avareza. A vida não consiste na abundância de bens. O dinheiro é servo, nunca senhor.
Sai ya ce musu, "Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba."
Gama inda dukiyarka take, a nan ne fa zuciyarka za tă kasance.
"Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’
Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace,
gama tabbatacce sukan yi fikafikai
sukan tashi sama kamar gaggafa.
Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki;
ka kasance da hikimar dainawa.
Duk mai ƙaunar kuɗi ba ya samun isashe;
duk ma ƙaunar dukiya ba ya ƙoshi da abin da yake samu.
Wannan ma ba shi da amfani.
Administrar com sabedoria
Honra ao Senhor com as tuas primícias. O sábio administra seus recursos com prudência e visão de eternidade.
Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka,
ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka;
Albarkar Ubangiji kan kawo wadata,
ba ya kuma ƙara wahala a kai.
Dukiyar da aka samu a hanyar da ba tă dace ba, ba ta da albarka,
amma adalci kan ceci mutum daga mutuwa.
Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri,
amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa.
Ya ma fi kyau ka sami hikima fiye da zinariya,
ka zaɓi fahimi a maimakon azurfa!
An fi son suna mai kyau fiye da wadata mai yawa;
tagomashi kuma ya fi azurfa ko zinariya.
Gara a kasance da kaɗan da tsoron Ubangiji
da a kasance da arziki mai yawa game da wahala.
Abin da mutum yake sha’awa shi ne ƙauna marar ƙarewa;
gara ka zama matalauci da ka zama maƙaryaci.
Ka kawar da ƙarya da kuma ƙarairayi nesa da ni;
kada ka ba ni talauci ko arziki,
amma ka ba ni abincina na yini kaɗai.
Perigos e armadilhas
Quem quer enriquecer cai em tentação. Fuja do amor ao dinheiro e busque contentamento no Senhor.
Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka.
Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu.
Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,
"Ba zan taɓa bar ka ba;
ba zan taɓa yashe ka ba."
Dukiya ba ta da amfani a ranar fushi,
amma adalci kan yi ceto daga mutuwa.
Dukiyar masu arziki ita ce birninsu mai katanga;
suna gani cewa ba za a iya huda katangar ba.
Tudo vem de Deus
De ti vem tudo, e das tuas mãos to damos. Os tributos são devidos — dai a César o que é de César e a Deus o que é de Deus.
"Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne.
Ku ba wa kowa hakkinsa. In kuna da bashin haraji, sai ku biya; in kuɗin shiga ne, ku biya kuɗin shiga; in ladabi ne, ku yi ladabi; in kuma girmamawa ne, ku ba da girma.
Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, gama hukumomin nan bayin Allah ne, waɗanda suke ba da dukan lokacinsu don aikin shugabanci.
Ƙanƙanen abin da mai adalci yake da shi
ya fi arzikin mugaye yawa;
gama za a kakkarya ikon mugaye,
amma Ubangiji zai riƙe mai adalci.
Na yi farin ciki da bin farillanka
yadda mutum yakan yi farin ciki da arziki mai yawa.