Doença
A doença é realidade humana que a Bíblia confronta com compaixão e poder. Jesus curou toda enfermidade e prometeu ouvir a oração da fé pelos enfermos.
Jesus, o curador
Jesus percorreu toda a Galileia curando toda enfermidade e doença entre o povo. Pelo seu nome, curas continuam acontecendo.
Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da matattu, ku tsabtacce kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta.
Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da matattu, ku tsabtacce kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta.
Da yamma ta yi, aka kawo masa masu aljanu da yawa, ya kuwa fitar da ruhohin ta wurin magana, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya. Wannan ya faru ne domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa,
"Ya ɗebi rashin lafiyarmu,
ya kuma ɗauki cututtukanmu."
da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.’
"Sa’an nan masu adalci za su amsa masa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha? Yaushe kuma muka gan ka baƙo muka karɓe ka, ko cikin bukatar tufafi muka yi maka sutura? Yaushe kuma muka gan ka cikin rashin lafiya ko a kurkuku muka ziyarce ka?’
"Sarkin zai amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’
Da jin wannan, Yesu ya ce musu, "Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. Ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi."
Ku warkar da marasa lafiya da suke wurin. Ku kuma faɗa musu cewa, ‘Mulkin Allah yana kusa da ku.’
Bayan da Yesu ya tara Sha Biyun wuri ɗaya, sai ya ba su iko da izini na fitar da dukan aljanu, da na warkar da cututtuka. Ya kuma aike su, su yi wa’azin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.
Promessas de cura
Eu sou o Senhor que te sara. As Escrituras prometem cura para o corpo e para a alma aos que confiam em Deus.
Ya ce, "In kun kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku kuka yi abin da yake daidai a idanunsa, in kun mai da hankali ga umarnansa, kuka kiyaye dukan farillansa, ba zan kawo muku wani ciwon da na kawo a kan Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku."
Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, albarkansa kuwa za tă kasance a kan abincinku da ruwan shanku. Zan ɗauke cuta daga cikinku.
Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, albarkansa kuwa za tă kasance a kan abincinku da ruwan shanku. Zan ɗauke cuta daga cikinku.
Ka warkar da ni, ya Ubangiji, zan kuwa warke;
ka cece ni zan kuwa cetu,
gama kai ne nake yabo.
wanda yake gafarta dukan zunubai
yake kuma warkar da dukan cututtuka,
Ya warkar da masu raunanar zuciya
ya ɗaɗɗaura miyakunsu.
Ubangiji yakan ba wa makafi ido,
Ubangiji yakan ɗaga waɗanda aka rusunar da su ƙasa,
Ubangiji yana ƙaunar masu adalci.
Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi;
Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala.
Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa;
zai albarkace shi a cikin ƙasar
ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba.
Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa
ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi.
Abokina ƙaunatacce, ina addu’a ka sami zaman lafiya don kome yă yi maka daidai, kamar yadda ruhunka yake zaune lafiya.
Oração pelos doentes
A oração da fé salvará o enfermo. Confessai as ofensas uns aos outros e orai uns pelos outros para serdes curados.
Akwai waninku da yake ciwo? Ya kamata yă kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu’a, su kuma shafa masa mai cikin sunan Ubangiji. Addu’ar da aka yi cikin bangaskiya, za tă warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa.
Akwai waninku da yake ciwo? Ya kamata yă kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu’a, su kuma shafa masa mai cikin sunan Ubangiji. Addu’ar da aka yi cikin bangaskiya, za tă warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa.
Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.
Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni. Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu. Amma ya ce mini, "Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona." Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni. Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.
Esperança na aflição
Ele tomou sobre si as nossas enfermidades. Mesmo na doença, o coração alegre serve de bom remédio e Deus dá esperança.
Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu
ya kuma daure da baƙin cikinmu
duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne,
ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba.
Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu
ya kuma daure da baƙin cikinmu
duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne,
ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba.
Mutane suka rena shi suka ƙi shi,
mutum ne cike da baƙin ciki, ya kuma saba da wahala.
Kamar wanda mutane suna ɓuya fuskokinsu daga gare shi
aka rena shi aka yi banza da shi.
Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau,
amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.
Sa rai da mutum ke yi kan taimake shi sa’ad da yake ciwo,
amma in ya karai, to, tasa ta ƙare.
Sa zuciyar da aka ɗaga zuwa gaba kan sa zuciya tă yi ciwo,
amma marmarin da aka ƙosar yana kamar itacen rai.
Sa’ad da na yi shiru,
ƙasusuwana sun yi ta mutuwa
cikin nishina dukan yini.
Kun san rashin lafiyar da na yi, shi ne ya yi mini hanyar da na kawo muku bishara da farko. Ko da yake ciwona gwaji ne gare ku, ba ku yi mini reni ko ƙyama ba. A maimakon haka, kuka karɓe ni sai ka ce mala’ikan Allah, kuma sai ka ce Kiristi Yesu kansa.
Ka daina shan ruwa kaɗai, yi amfani da ruwan inabi kaɗan saboda cikinka da kuma yawan rashin lafiyarka.
Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe."