Ensinar
Ensinar é mandamento e dom. A Bíblia exorta pais, líderes e mestres a transmitir a verdade divina com fidelidade, paciência e sabedoria para as próximas gerações.
Ensinar a Palavra
Toda Escritura é útil para ensinar. Quem ouve as palavras de Jesus e as pratica é como o homem sábio que construiu sobre a rocha.
Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci, domin mutumin Allah yă zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.
"Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse.
Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah.
Gama duk abin da aka rubuta a dā an rubuta ne domin yă koya mana, don ta wurin jimrewa da kuma ƙarfafawar Nassosi mu kasance da bege.
Karin maganar Solomon ɗan Dawuda, sarkin Isra’ila.
Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo;
don ganewa kalmomi masu zurfi;
don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali,
kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace;
don sa marar azanci yă yi hankali,
yă sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa,
bari masu hikima su saurara, su kuma ƙara ga saninsu,
bari masu tunani kuma su sami jagora,
don su fahimci karin magana da kuma misalai,
kalmomi da kuma kacici-kacici masu hikima.
Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,
amma wawaye sun rena hikima da horo.
Instruir as gerações
Ensina a criança nos caminhos de Deus. A geração que não conhece o Senhor perde a herança espiritual da fé.
Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku. Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.
Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka
kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
Za su zama kayan ado don su inganta ka
da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.
Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka
kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
Ka ɗaura su a zuciyarka har abada;
ka ɗaura su kewaye da wuyanka.
Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka;
sa’ad da kake barci, za su lura da kai;
sa’ad da ka farka, za su yi maka magana.
Gama waɗannan umarnai fitila ne,
wannan koyarwa haske ne,
kuma gyare-gyaren horo
hanyar rayuwa ce,
Ka nemi hikima, ka nemi fahimi;
kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su.
Kada ka ƙyale hikima, za tă kuwa tsare ka;
ka ƙaunace ta, za tă kuwa lura da kai.
Hikima ce mafi girma duka; saboda haka ka nemi hikima.
Ko da za tă ci duk abin da kake da shi, ka dai nemi fahimi.
Ka ƙaunace ta, za tă ɗaukaka ka;
ka rungume ta, za tă kuwa girmama ka.
Ka riƙe umarni, kada ka bari yă kuɓuce;
ka tsare shi sosai, gama ranka ne.
Kada ka sa ƙafa a kan hanyar mugaye
kada ka bi gurbin mugaye.
Fiye da kome duka, ka tsare zuciyarka,
gama maɓulɓulan ruwan rijiyar rai ne.
Ka kau da muguwar magana daga bakinka;
ka yi nesa da magana marar kyau daga leɓunanka.
Bari idanunka su dubi gaba sosai,
ka kafa idanunka kai tsaye a gabanka.
Ka san inda ƙafafunka suke takawa
ka bi hanyoyin da suke daram kawai.
Kada ka kauce dama ko hagu;
ka kiyaye ƙafarka daga mugunta.
Koyarwar mai hikima maɓulɓulan rai ne,
mai juyar da mutum daga tarkon mutuwa.
"Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima,
sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.
Ya mutanena, ku ji koyarwata;
ku saurari kalmomin bakina.
Zan buɗe bakina da misalai,
zan faɗi ɓoyayyun abubuwa, abubuwan dā,
abin da muka ji muka kuma sani,
abubuwan da kakanninmu suka faɗa mana.
Ba za mu ɓoye su wa ’ya’yanmu ba;
za mu faɗa wa tsara mai zuwa
ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji,
ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata.
Bayan tsaran nan duka suka rasu, sai wata tsara ta taso wadda ba tă san Ubangiji ko abin da ya yi wa Isra’ila ba.
Fidelidade no ensino
Quem ensina com fidelidade merece dupla honra. Cuidado com doutrinas falsas — permaneçam na doutrina de Cristo.
Dattawan da suka bi da al’amuran ikkilisiya da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman waɗanda aikinsu wa’azi ne da kuma koyarwa. Gama Nassi ya ce, "Kada ka sa wa bijimi takunkumi yayinda yake sussukar hatsi," da kuma, "Ma’aikaci ya cancanci hakkinsa."
Ka yi nesa da maganganun banza na rashin tsoron Allah, gama waɗanda suka mai da hankali ga yin waɗannan za su ƙara zama marasa tsoron Allah. Koyarwarsu za tă bazu kamar ruɓaɓɓen gyambo. A cikinsu akwai Himenayus da Filetus,
Duk mutumin da bai tsaya a kan koyarwar Kiristi ba, amma ya yi ƙari a kanta, mutumin nan ba shi da Allah. Amma wanda ya tsaya a kan koyarwar Kiristi, yana da Uban da kuma Ɗan.
Sai bayan da aka kai tsakiyar Bikin, sa’an nan Yesu ya haura zuwa filin haikali ya fara koyarwa. Yahudawa suka yi mamaki suna tambaya, "Yaya wannan mutum ya sami wannan sani haka ba tare da ya yi wani karatu ba?"
Yesu ya amsa ya ce, "Koyarwata ba tawa ba ce, ta fito ne daga wurin wanda ya aiko ni. Duk wanda ya zaɓi yin nufin Allah, zai gane ko koyarwata daga Allah ce, ko kuwa don kaina ne nake magana. Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi.