Pular para o conteúdo
Publicidade

Família

Por Bíblia Online

A família é a primeira instituição criada por Deus. Ele a projetou para ser escola de amor, fé e formação de caráter. A Bíblia honra a família e nos ensina a cuidar dela.

Eu e minha casa

Eu e minha casa serviremos ao Senhor. A família que serve a Deus juntos permanece unida e fortalecida em todas as circunstâncias.

Amma in kuka ga ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, sai ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa, ko allolin da kakanninku suka bauta musu a hayin Kogin Yuferites, ko kuma allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a cikin ƙasarsu. Amma da ni da gidana, Ubangiji ne za mu bauta wa."

Amma in kuka ga ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, sai ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa, ko allolin da kakanninku suka bauta musu a hayin Kogin Yuferites, ko kuma allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a cikin ƙasarsu. Amma da ni da gidana, Ubangiji ne za mu bauta wa."

Suka amsa suka ce, "Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka."

Bari Ubangiji Allah kasance tare da mu kamar yadda ya kasance da kakanninmu; kada taɓa rabu da mu, ko yashe mu.

Criar os filhos

Instrui a criança no caminho em que deve andar. O lar é a primeira escola de fé e obediência.

Ka hori yaro a hanyar da ya kamata bi,

kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.

Ka hori yaro a hanyar da ya kamata bi,

kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.

Jan kunne game da jaraba

Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka

kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

Za su zama kayan ado don su inganta ka

da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.

Gargaɗi a kan zina

Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka

kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. Ku koya wa ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.

Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. Ku koya wa ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.

Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.

Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.

Ya’ya da iyaye

Ku ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, "Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,

Honrar e amar

Honra teu pai e tua mãe. A família funciona com perdão, paciência e amor incondicional entre todos os seus membros.

Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, ka kuma ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka."

Kashen aure

Sa’ad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai ya bar Galili, ya tafi yankin Yahudiya a ɗaya gefen Urdun. Taron mutane mai yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da su a can.

Waɗansu Farisiyawa suka zo wurinsa don su gwada shi. Suka yi tambaya suka ce, "Daidai ne mutum saki matarsa saboda wani dalili da kuma a kan kowane dalili?"

Ya amsa ya ce, "Ba ku taɓa karantawa ba ne cewa, a farkon halitta, Mahalicci ya yi su namiji da ta mace, ya kuma ce, Saboda wannan dalili, namiji zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa manne wa matarsa, biyun kuwa su zama jiki guda? Ta haka, ba sa ƙara zama biyu, sai dai ɗaya. Saboda haka abin da Allah ya haɗa fa, kada mutum raba."

Suka yi tambaya, suka ce, "To, me ya sa Musa ya umarta cewa mutum ba wa matarsa takardar saki, kuma kore ta?"

Yesu ya amsa ya ce, "Musa ya ba ku izini ku saki matanku saboda taurin zuciyarku ne. Amma ba haka yake ba daga farko. Ina faɗa muku cewa duk wanda ya saki matarsa, sai dai a kan rashin aminci a cikin aure, ya kuwa auri wata, ya yi zina ke nan."

Almajiran suka ce masa, "In haka yake tsakanin miji da mata, ashe, ya ma fi kyau kada a yi aure."

Yesu ya ce, "Ba kowa ba ne zai yarda da wannan magana, sai dai waɗanda aka yarda musu. Gama waɗansu bābānni ne domin haka aka haife su; waɗansu kuwa mutane ne suka mai da su haka; waɗansu kuma sun ƙi aure ne saboda mulkin sama. Duk mai iya ɗaukar wannan ɗauka."

Yesu da ƙananan yara

Sa’an nan aka kawo yara ƙanana wurin Yesu don ɗibiya musu hannuwansa, kuma yi musu addu’a. Amma almajirai suka tsawata wa waɗanda suka kawo su.

Yesu ya ce, "Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin sama na irin waɗannan ne." Sa’ad da ya ɗibiya musu hannuwansa, sai ya tafi abinsa.

Saurayi mai arziki

To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, "Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?"

Yesu ya amsa ya ce, "Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan."

Mutumin ya yi tambaya ya ce, "Waɗanne?"

Yesu ya amsa ya ce, " Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, ka kuma ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka."

Saurayin ya ce, "Duk waɗannan na kiyaye. Me kuma ya rage mini?"

Yesu ya amsa ya ce, "In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni."

Da saurayin ya ji haka, sai ya tafi rai a ɓace, don yana da arziki sosai.

Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, "Gaskiya nake gaya muku, yana da wuya mai arziki shiga mulkin sama. Har wa yau ina gaya muku, zai fi sauƙi raƙumi shiga ta kafar allura, da mai arziki shiga mulkin Allah."

Sa’ad da almajiran suka ji wannan, sai suka yi mamaki ƙwarai. Suka yi tambaya suka ce, "To, wa zai sami ceto ke nan?"

Yesu ya kalle su ya ce, "Ga mutum kam, wannan ba ya yiwuwa, amma ga Allah kuwa, dukan abubuwa masu yiwuwa ne."

Sai Bitrus ya amsa masa, "Ga shi mun bar kome don mu bi ka! Me za mu samu ke nan?"

Yesu ya ce musu, "Gaskiya nake gaya muku, a lokacin sabunta dukan kome, sa’ad da Ɗan Mutum ya zauna a kan kursiyinsa mai daraja, ku da kuka bi ni, ku ma za ku zauna a kan kursiyoyi goma sha biyu, kuna yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a. Duk kuma wanda ya bar gidaje ko yan’uwa maza ko yan’uwa mata ko mahaifi ko mahaifiya ko yara ko gonaki, saboda ni, zai sami abin da ya fi haka riɓi ɗari, kuma gāji rai madawwami. Amma da yawa da suke na farko, za su zama na ƙarshe, da yawa kuma da suke na ƙarshe, za su zama na farko.

Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.

Duk da haka, dole kowannenku ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar yi biyayya ga mijinta.

Duk wanda ya ce, "Ina ƙaunar Allah," amma yana ƙin ɗan’uwansa, maƙaryaci ne. Gama duk wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa da yake gani, ba zai iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba.

Cuidar da família

Quem não cuida dos seus negou a fé. A família é responsabilidade sagrada — prover, proteger e abençoar é mandamento divino.

In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.

In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.

Amma in gwauruwa tana da ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah.

Tsattsaguwa cikin ikkilisiya

Ina roƙonku yan’uwa, a cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, dukanku ku yarda da juna, domin kada a sami tsattsaguwa a cikinku, domin kuma ku zama ɗaya, cikakku a cikin halinku da tunaninku.

Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,

yara lada ne daga gare shi.

Kamar kibiyoyi a hannun jarumi

haka ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.

Mai albarka ne mutumin

da korinsa sun cika da su.

Ba za a kunyata su ba

sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

Amma daga madawwami zuwa madawwami

ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa,

adalcinsa kuma tare da ya’yansu,

tare da waɗanda suke kiyaye alkawarinsa

suna kuma tuna su yi biyayya da farillansa.

Amma daga madawwami zuwa madawwami

ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa,

adalcinsa kuma tare da ya’yansu,

tare da waɗanda suke kiyaye alkawarinsa

suna kuma tuna su yi biyayya da farillansa.

Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma

sa’ad da yan’uwa suna zaman lafiya!

Unidade familiar

A coroa dos velhos são os filhos dos filhos. O casamento, os filhos e a comunhão familiar são bênçãos de Deus.

Jikoki rawanin tsofaffi ne,

kuma iyaye su ne abin taƙamar ya’yansu.

Jikoki rawanin tsofaffi ne,

kuma iyaye su ne abin taƙamar ya’yansu.

Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe,

ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi.

Mutum mai abokai masu yawa kan lalace,

amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa.

Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka,

kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka,

gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa.

Faɗi 14

Ɗana, in zuciyarka mai hikima ce,

to, zuciyata za yi murna;

Mahaifin adali yana da farin ciki sosai;

duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa.

Karin maganar Solomon.

Ɗa mai hikima yakan kawo wa mahaifinsa farin ciki,

amma wawan ɗa kan sa wa mahaifiyarsa baƙin ciki.

Ka gama aikinka

ka kuma shirya gonakinka;

bayan haka, ka gina gidanka.

Mutum mai haɗama kan kawo wahala ga iyalinsa,

amma wanda yake ƙin cin hanci zai rayu.

Duk wanda ya kawo wahala wa iyalinsa zai gāji iska kawai,

kuma wawa zai zama bawan masu hikima.

Casamento e família

O homem deixará pai e mãe e se unirá à sua mulher. A família começa no casamento — aliança sagrada diante de Deus.

Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, "Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa."

Ka more rayuwa da matarka, wadda kake ƙauna, dukan kwanakin nan marasa amfani da Allah ya ba ka a duniya. Gama wannan ne rabonka a rayuwa da kuma na faman aikinka a duniya.

Amma a farkon halitta, Allah ya halicce su miji da mace. Saboda wannan dalili, mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, manne wa matarsa, su biyun kuma za su zama jiki ɗaya. Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya. Domin haka, abin da Allah ya haɗa, kada mutum raba."

In fa haka ne, ko da yake ku mugaye ne, kun san ba ya’yanku kyautai masu kyau, balle fa Ubanku na sama, zai yi fiye da haka, ta wurin ba da Ruhu Mai Tsarki, ga masu roƙonsa!"

"Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta

ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa?

Mai yiwuwa ta manta,

amma ba zan taɓa manta da ke ba!

Duba, na zāna ki a tafin hannuwana;

katangarki kullum suna a gabana.

Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake. Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.

Seja o primeiro