Filhos
Os filhos são herança do Senhor — bênção e responsabilidade sagrada. A Bíblia orienta sobre a criação dos filhos com amor, disciplina e instrução nos caminhos de Deus.
Herança do Senhor
Os filhos são herança do Senhor e o fruto do ventre é seu galardão. Bem-aventurado o homem que enche deles a sua aljava.
’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,
yara lada ne daga gare shi.
Kamar kibiyoyi a hannun jarumi
haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.
Mai albarka ne mutumin
da korinsa sun cika da su.
Ba za a kunyata su ba
sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.
Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji,
waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.
Za ka ci amfanin aikinka;
albarku da wadata za su zama naka.
Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya
a cikin gidanka;
’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun
kewaye da teburinka.
Ta haka mai albarka yake
wanda yake tsoron Ubangiji.
Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji,
waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.
Za ka ci amfanin aikinka;
albarku da wadata za su zama naka.
Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya
a cikin gidanka;
’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun
kewaye da teburinka.
Ta haka ’ya’yanmu maza a ƙuruciyarsu
za su zama kamar tsire-tsiren da aka kula da su,
’ya’yanmu mata kuma za su zama kamar ginshiƙai
da sassaƙa don adon fada.
’Ya’yansa za su zama manya a ƙasar;
tsaran masu aikata gaskiya za su sami albarka.
Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, "Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa."
’Ya’yanku za su zama masu albarka, haka ma hatsin gonakinku da kuma ’ya’yan dabbobinku, wato, ’ya’yan shanu da ’yan tumakinku.
Za a albarkace ku fiye da waɗansu mutane; babu wani cikin maza ko matanku da zai kasance babu haihuwa, ba kuwa wata dabbarku da za tă kasance babu haihuwa.
Instruir e disciplinar
Instrui a criança no caminho em que deve andar, e quando envelhecer não se desviará dele. Disciplina é amor em ação.
Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi,
kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.
Wauta tana da yawa a zuciyar yara,
amma sandar horo zai kore ta nesa da su.
Duk wanda ba ya horon ɗansa ba ƙaunarsa yake yi ba,
amma duk mai ƙaunarsa yakan kula ya hore shi.
Sandar gyara kan ba da hikima,
amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa.
Kada ka bar yaro ba horo;
in ka yi masa horo da sanda, ba zai mutu ba.
Ku saurara ’ya’yana ga koyarwar mahaifinku;
ku mai da hankali, ku sami fahimi.
Karin maganar Solomon.
Ɗa mai hikima yakan kawo wa mahaifinsa farin ciki,
amma wawan ɗa kan sa wa mahaifiyarsa baƙin ciki.
Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.
O amor de Deus por crianças
Deixai vir a mim as crianças. Jesus acolheu, abençoou e honrou as crianças como modelo de fé e humildade.
Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi, ya ce musu, "Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.
In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ’ya’yanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba!
Yesu kuwa ya yi girma, ya kuma ƙaru cikin hikima, ya kuma sami tagomashi a wurin Allah da mutane.
Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa,
haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa;
Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba.
Bênção e promessa
O Senhor te abençoe e te guarde. Os filhos dos justos serão abençoados e suas gerações caminharão na retidão.
" ‘ "Ubangiji yă albarkace ku,
yă kuma kiyaye ku;
Ubangiji yă sa fuskarsa ta haskaka a kanku,
yă kuma yi muku alheri;
Ubangiji yă dube ku da idon rahama,
yă kuma ba ku salama." ’
Allah yă ba ka daga raɓar sama da kuma yalwar ƙasa,
yalwar hatsi da sabon ruwan inabi.
Bari al’ummai su bauta maka mutane kuma su rusuna maka.
Ka zama shugaba a kan ’yan’uwanka
bari kuma ’ya’yan mahaifiyarka su rusuna maka.
Bari waɗanda suka la’anta ka, su la’antu;
waɗanda kuma suka sa maka albarka, su sami albarka."
Gama zan zuba ruwa a ƙeƙasasshiyar ƙasa,
rafuffuka kuma a busasshiyar ƙasa;
zan ba da Ruhuna ga ’ya’yanka,
albarkata kuma ga zuriyarka.
Za su tsiro kamar ciyawa a wuriyar ruwa,
kamar kurmi kusa da rafuffuka masu gudu.
Ubangiji zai koya wa dukan ’ya’yanki maza,
da girma kuma salamar ’ya’yanki zai zama.
"Kafin in siffanta ka a cikin ciki na san ka,
kafin a haife ka, na keɓe ka;
na naɗa ka ka zama annabi ga al’ummai."
Za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu. Zan ba su zuciya ɗaya da aiki ɗaya, don kullum su ji tsorona domin amfaninsu da kuma amfanin ’ya’yansu a bayansu.
Gama ka halicci ciki-cikina;
ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.
Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;
ayyukanka suna da banmamaki,
na san da haka sosai.
Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba
sa’ad da aka yi ni asirce.
Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.
Idanunka sun ga jikina marar fasali;
dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka
kafin ɗayansu yă kasance.
Daga haihuwa an jefa ni a kanka;
daga cikin mahaifiyata kai ne Allahna.
Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa,
duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba
ko a ce ’ya’yansu suna roƙon burodi.
Kullum suna bayar hannu sake suna kuma ba da bashi ba da wahala ba,
za a yi wa ’ya’yansu albarka.
Ba za mu ɓoye su wa ’ya’yanmu ba;
za mu faɗa wa tsara mai zuwa
ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji,
ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata.
Jikoki rawanin tsofaffi ne,
kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu.
Mai adalci kan yi rayuwa marar abin zargi;
masu albarka ne ’ya’yan da za su biyo bayansa.
Criação e obediência
Pais, criai vossos filhos na disciplina e instrução do Senhor. Filhos, obedecei a vossos pais — isto é justo e agradável a Deus.
Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, "Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya."
Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.
’Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji.
Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.
Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa? In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ’ya’yan gida ba.
Amma in gwauruwa tana da ’ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah.
Macen da za tă haihu takan yi naƙuda domin lokacinta ya yi; amma sa’ad da ta haihu, sai ta manta da wahalar domin farin ciki an haifi jariri a duniya.
Amma ’ya’yanku ƙanana waɗanda ba su san mugunta ko nagarta ba, waɗanda kuke tsammani za a kwashe su ganima, su za su shiga ƙasar. Zan ba da ita gare su, za su kuwa mallake ta.