Publicidade

Salmos 128

Waƙar haurawa.

1 Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji,

waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.

2 Za ka ci amfanin aikinka;

albarku da wadata za su zama naka.

3 Matarka za zama kamar kuringar inabi mai ya’ya

a cikin gidanka;

ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun

kewaye da teburinka.

4 Ta haka mai albarka yake

wanda yake tsoron Ubangiji.

5 Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona

dukan kwanakin ranka;

bari ka ga wadatar Urushalima,

6 bari kuma ka rayu ka ga ya’ya ya’yanka.

Salama kasance tare da Isra’ila.

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-