Pular para o conteúdo
Publicidade

Homem de Deus

Por Bíblia Online

O homem de Deus é aquele que busca a justiça, a piedade, a fé e o amor. A Bíblia apresenta modelos de homens íntegros que andaram com Deus e marcaram a história.

Características do homem de Deus

O homem de Deus foge das paixões e segue a justiça, a piedade, a fé, o amor, a perseverança e a mansidão.

Umarnin Bulus ga Timoti

Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali.

Kada ka bar wani rena ka domin kai matashi ne, sai dai ka zama gurbi ga masu bi cikin magana, cikin rayuwa, cikin ƙauna, cikin bangaskiya da kuma cikin zaman tsarki.

Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi. Ku yi kome da ƙauna.

Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau.

Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa

shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai

ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.

Exemplos bíblicos

Noé era justo e íntegro entre seus contemporâneos. Jó era homem reto que temia a Deus e se desviava do mal.

Ga tarihin Nuhu.

Nuhu mutum ne mai adalci, marar abin zargi a cikin mutanen zamaninsa, ya kuma yi tafiya tare da Allah.

Gabatarwa

A ƙasar Uz akwai wani mutum mai suna Ayuba. Mutum ne marar laifi kuma mai adalci; yana tsoron Allah, ba ruwansa da mugunta.

Akwai wani mutumin da aka aiko daga Allah; mai suna Yohanna. Ya zo a matsayin mai shaida domin ba da shaida game da wannan haske, don ta wurinsa dukan mutane su ba da gaskiya.

Mutum mai basira kan kafa idonsa a kan hikima,

amma idanun wawa suna a kan ƙarshen duniya.

Viver como filho de Deus

Quem faz a vontade de Deus é eleito. Medite na Palavra e ande nos caminhos do Senhor como verdadeiro discípulo.

Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ya’yan Allah ya’yan da aka haifa ba bisa hanyar yan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah.

Mun san cewa Allah ba ya sauraron masu zunubi. Yakan saurari mai tsoronsa mai aikata nufinsa.

Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta?

Sai ta yin rayuwa bisa ga maganarka.

Na neme ka da dukan zuciyata;

kada ka bar ni in kauce daga umarnanka.

Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata

don kada in yi maka zunubi.

Yabo ya tabbata gare ka, ya Ubangiji;

ka koya mini ƙa’idodinka.

Da leɓunana na ba da labarin

dukan dokokin da suka fito bakinka.

Na yi farin ciki da bin farillanka

yadda mutum yakan yi farin ciki da arziki mai yawa.

Na yi tunani a kan farillanka

na kuma lura da hanyoyinka.

Na yi murna a cikin ƙa’idodinka;

ba zan ƙyale maganarka ba.

ג Gimel

Mai farin ciki ne mutumin

da ba ya aiki da shawarar mugaye

ko yi abin da masu zunubi suke yi

ko zauna tare da masu yin ba’a.

Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji,

kuma yana ta nazarinta dare da rana.

Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa,

wanda yake ba da amfani a daidai lokaci

wanda kuma ganyensa ba sa bushewa.

Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.

Ba haka yake da mugaye ba!

Su kamar yayi ne

da iska take kwashewa.

Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba,

balle a sami masu zunubi a taron adalai.

Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa,

amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.

sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta , wadda take lalacewa saboda sha’awace-shaawacen da suke ruɗe ku. A maimakon haka, bari Ruhu sabunta tunaninku da kuma halayenku. Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, bayyana cikin adalci, da zaman tsarki.

Seja o primeiro