Intimidade com Deus
A intimidade com Deus é o maior privilégio do cristão. Ele nos convida a nos aproximar, a conhecê-lo profundamente e a desfrutar de comunhão diária com o Criador do universo.
Aproximar-se de Deus
Chegai-vos a Deus e Ele se chegará a vós. Deus deseja intimidade, não religiosidade. Ele busca os que o buscam de todo coração.
Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.
"Ku zo, dukanku masu jin ƙishi,
ku zo wurin ruwaye;
ku kuma da ba ku da kuɗi,
ku zo, ku saya ku kuma ci!
Ku zo, ku saya ruwan inabi da madara
ba tare da kuɗi ba ba za ku kuma biya kome ba.
Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba,
ku kuma yi wahala a kan abin da ba za ku ƙoshi ba?
Ku saurara, ku saurare ni, ku kuma ci abin da yake da kyau,
ranku kuma zai ji daɗin abinci mafi kyau.
Ku kasa kunne ku kuma zo gare ni;
ku saurare ni, don ranku ya rayu.
Zan yi madawwamin alkawari da ku,
zan nuna muku ƙaunata marar ƙarewa da na yi wa Dawuda alkawari.
Duba, na mai da shi shaida ga mutane,
shugaba da kuma jagorar mutane.
Tabbatacce za ku kira al’umman da ba ku sani ba,
kuma al’umman da ba ku sani ba za su sheƙo a guje zuwa wurinku,
saboda Ubangiji Allahnku,
Mai Tsarkin nan na Isra’ila,
gama ya darjanta ku."
Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa;
ku yi kira gare shi tun yana kusa.
Kafin su yi kira zan amsa;
yayinda suke cikin magana zan ji.
‘Kira gare ni zan kuwa amsa maka in kuma faɗa maka manyan abubuwan da ba a iya kaiwa, da ba ka sani ba.’
Gama na san shirye-shiryen da na yi muku," in ji Ubangiji, "shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.
Sede de Deus
Como a corça deseja as correntes de água, assim a minha alma suspira por ti, ó Deus. A intimidade nasce do desejo profundo.
Kamar yadda barewa take marmarin ruwan rafuffuka,
haka raina yake marmarinka, ya Allah.
Raina yana ƙishin Allah, Allah mai rai.
Yaushe zan tafi in sadu da Allah ne?
Ya Allah, kai ne Allahna,
da nacewa na neme ka;
raina yana ƙishinka,
jikina yana marmarinka,
cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye
inda babu ruwa.
Na gan ka a wuri mai tsarki
na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka.
Domin ƙaunarka ta fi rai kyau,
leɓunana za su ɗaukaka ka.
Zan yabe ka muddin raina,
kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.
Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau;
da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka.
A gadona na tuna da kai;
ina tunaninka dukan dare.
Domin kai ne mai taimakona,
ina rera a cikin inuwar fikafikanka.
Raina ya manne maka;
hannunka na dama yana riƙe da ni.
Su da suke neman raina za su hallaka;
za su gangara zuwa zurfafan duniya.
Za a bayar da su ga takobi
su kuma zama abincin karnukan jeji.
Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah;
dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi,
amma za a rufe bakunan maƙaryata.
Unidade com o Pai
Jesus orou pela unidade dos seus com o Pai. A intimidade com Deus inclui confissão, perdão e alegria na comunhão.
Na ba su ɗaukakar da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya. Ni a cikinsu kai kuma a cikina. Bari su kasance da cikakken haɗinkai, domin duniya ta san cewa kai ka aiko ni. Ka kuwa ƙaunace su yadda ka ƙaunace ni.
Ubangiji Allahnki yana tare da ke,
mai iko ne don ceto.
Zai yi matuƙar farin ciki da ke,
zai rufe ki da ƙaunarsa,
zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa."
In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.