Publicidade

Jovens

Por Bíblia Online

Deus tem planos maravilhosos para os jovens. A Bíblia os convida a consagrar a juventude ao Senhor, crescer em sabedoria e ser exemplo para todos em fé, palavra, conduta e amor.

Ninguém despreze a tua mocidade

Paulo exortou Timóteo: sê exemplo dos fiéis na palavra, no procedimento, no amor, no espírito, na fé e na pureza.

Kada ka bar wani rena ka domin kai matashi ne, sai dai ka zama gurbi ga masu bi cikin magana, cikin rayuwa, cikin ƙauna, cikin bangaskiya da kuma cikin zaman tsarki.

Haka kuma, ka ƙarfafa samari su zama masu kamunkai.

Ya’ya da iyaye

Ku ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, "Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya."

Ya’ya da iyaye

Ku ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, "Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,

Lembrar do Criador na juventude

Lembra-te do teu Criador nos dias da tua mocidade. A sabedoria ganha cedo produz frutos duradouros na vida inteira.

Ka tuna da Mahaliccinka

a kwanakin ƙuruciyarka,

kafin lokacin wahala ta zo

shekaru kuma su ƙarato sa’ad da za ka ce,

"Ba na jin daɗinsu,"

Ka tuna da Mahaliccinka

a kwanakin ƙuruciyarka,

kafin lokacin wahala ta zo

shekaru kuma su ƙarato sa’ad da za ka ce,

"Ba na jin daɗinsu,"

kafin rana da haske

wata da taurari su daina haske,

gizagizai kuma su tattaru bayan da suka sheƙa ruwa;

sa’ad da masu tsaron gida suke rawar jiki,

majiya ƙarfi kuma suka rasa ƙarfi,

sa’ad da masu niƙa suka daina don ba su da yawa,

idanun da suke duba ta taga suka duhunta;

Ka yi murna, kai matashi, a ƙuruciyarka,

bari zuciyarka kuma yi farin ciki a kwanakin ƙuruciyarka.

Ka bi shawarar zuciyarka

da kuma duk abin da idanunka suka gani,

amma ka sani fa, cikin dukan al’amuran nan

Allah zai shari’anta ka.

Saboda haka, ka fid da tsoro daga zuciyarka

ka kakkaɓe duk wani abin da ya dami rayuwarka,

gama ƙuruciya da ƙarfi ba su da amfani.

Cin gaba ba shi da amfani

Gara saurayi wanda yake matalauci amma yake da hikima da sarkin da ya tsufa mai wauta, wanda ba ya karɓar shawara.

Força e promessa

Os jovens renovam suas forças quando esperam no Senhor. Deus levanta jovens com visões e sonhos para transformar o mundo.

Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,

samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;

amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji

za su sabunta ƙarfinsu.

Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;

za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,

za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.

Ranar Ubangiji

"Daga baya kuma,

zan zuba Ruhuna a bisan dukan mutane.

Ya’yanku maza da mata za su yi annabci,

tsofaffinku za su yi mafarkai,

matasanku za su ga wahayoyi.

Har ma a bisan bayina, maza da mata,

zan zuba Ruhuna a kwanakin nan.

Ga samarin nan guda huɗu Allah ya ba su sani da ganewar dukan irin littattafai da kuma koyarwa. Daniyel kuma ya iya gane wahayi da kowane irin mafarki.

A ƙarshen lokacin da sarki ya sa da za a kawo su ciki, sai sarkin fada ya gabatar da su ga Nebukadnezzar. Sarki kuwa ya yi magana da su, sai ya gano cewa babu wani kamar Daniyel, Hananiya, Mishayel da kuma Azariya; don haka sai suka shiga yi wa sarki hidima.

Ɗaukakar matasa maza ita ce ƙarfinsu,

furfura ita ce darajar tsofaffi.

Akan san ƙananan yara ta ayyukansu,

ana iya sani ko rayuwarsu amintattu ne, mai nagarta.

Guardar o caminho

Como purificará o jovem seu caminho? Guardando-o segundo a tua Palavra. A Escritura na juventude guarda do pecado a vida inteira.

Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta?

Sai ta yin rayuwa bisa ga maganarka.

Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata

don kada in yi maka zunubi.

Gama kai ne abin sa zuciyata, ya Ubangiji Mai Iko Duka,

ƙarfin zuciyata tun ina yaro.

samari da yan mata,

tsofaffi da yara.

Bari su yabi sunan Ubangiji,

gama sunansa ne kaɗai mafi ɗaukaka;

darajarsa ta fi ƙarfin duniya da sammai.

Karin maganar Solomon ɗan Dawuda, sarkin Isra’ila.

Ga karin magana da za su taimake ka don samun hikima da horo;

don ganewa kalmomi masu zurfi;

don neman rayuwa ta horo da kuma ta hankali,

kana yin abin da yake daidai, mai adalci da kuma wanda ya dace;

don sa marar azanci yi hankali,

sa matasa su sani, su kuma iya rarrabewa,

Faɗi 16

Ka saurara, ɗana, ka zama mai hikima,

ka kafa zuciyarka a hanyar da take daidai.

Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa

ko masu haɗama kansu da abinci,

gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta,

gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.

Faɗi 17

Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai,

kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa.

Coragem e vocação

Deus chamou jovens como Jeremias e Josué para grandes missões. A juventude não é desculpa — é oportunidade de servir poderosamente.

Sai na ce, "Kayya, Ubangiji Mai Iko Duka, ban iya magana ba; ni ɗan yaro ne kawai."

Amma Ubangiji ya ce mini, "Kada ka ce, Ni ɗan yaro ne kawai.Dole ka je wurin kowane mutumin da na aike ka ka kuma faɗa abin da na umarce ka. Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da kai kuma zan kiyaye ka," in ji Ubangiji.

Gama na san shirye-shiryen da na yi muku," in ji Ubangiji, "shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba. Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku. Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku. Za ku same ni," in ji Ubangiji, "zan kuma komo da ku daga bauta. Zan tattaro ku daga dukan al’ummai in sa ku inda na kore ku," in ji Ubangiji, "zan kuma komo da ku zuwa wurin da na kwashe ku zuwa zaman bauta."

Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, ka yi lura fa, ka yi biyayya da dokokin da bawana Musa ya ba ka; kada ka kauce ga bin dokokin ko hagu ko dama, domin ka yi nasara a duk, inda za ka je. Kada ka bar Littafin Dokokin nan rabu da bakinka, sai dai ka yi ta tunani game da shi dare da rana, don ka lura, ka yi duk abin da aka rubuta a ciki, ta haka ne za ka yi nasara cikin duk abin da za ka yi. Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je."

Samari, ku ma, ku yi biyayya ga waɗanda suka girme ku. Dukanku, ku yafa sauƙinkai ga juna, domin,

"Allah yana gāba da mai girman kai,

amma yakan yi alheri ga mai sauƙinkai."

Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama.

Ina rubuta muku, ya’yana ƙaunatattu,

domin kun san Uba.

Ina rubuta muku, ubanni,

domin kun san shi wanda yake tun farko.

Ina rubuta muku, samari,

domin kuna da ƙarfi,

maganar Allah kuwa tana zaune a cikinku,

kun kuma ci nasara a kan mugun nan.

Bari mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa ba, ba cikin fasikanci da rashin kunya ba, ba kuma cikin faɗa da kishi ba.

Yana da kyau mutum sha wuya

tun yana yaro.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-