Pular para o conteúdo
Publicidade

Justiça

Por Bíblia Online

A justiça é atributo de Deus e vocação do cristão. A Bíblia chama os crentes a buscar a justiça, praticar o que é reto e confiar no Deus que julga justamente.

Buscar a justiça

Buscai primeiro o Reino de Deus e a sua justiça. Quem semeia justiça colherá galardão seguro e duradouro.

Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa.

Mugun mutum kan sami albashin ƙarya

amma shi da ya shuka adalci zai girbe lada tabbatacce.

Duk wanda ya nemi adalci da ƙauna

kan sami rai, wadata da girmamawa.

Yin abin da yake daidai da kuma nagari

Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya.

Mutum zai yi tunani hanyoyinsa daidai suke,

amma Ubangiji yakan auna zuciya.

Dukiyar da aka samu a hanyar da ba dace ba, ba ta da albarka,

amma adalci kan ceci mutum daga mutuwa.

Justiça em Cristo

Deus tornou Cristo a nossa justiça. Pela fé somos declarados justos diante de Deus — não por obras, mas pela graça.

Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi kamar hadayar zunubi saboda mu, domin mu sami adalcin Allah ta wurinsa.

Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane. Yana koya mana mu ce, "A’a" ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-shaawacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani,

Umarnin Bulus ga Timoti

Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali.

A ƙarshe, yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan.

Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne.

Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba.

Praticar a justiça

O fruto da justiça semeia-se em paz para os que promovem a paz. Os olhos do Senhor estão sobre os justos.

Masu salama da suke shuki cikin salama sukan girbe adalci.

Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.

Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.

Gama Ubangiji yana ƙaunar masu aikata daidai

kuma ba zai yashe amintattunsa ba.

Za a hallaka masu aikata mugunta gaba ɗaya,

ya’yan mugaye za su hallaka.

Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci

kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;

Tabbatacce ba zai taɓa jijjigu ba;

za a tuna da mai adalci har abada.

Mai farin ciki ne mutumin

da ba ya aiki da shawarar mugaye

ko yi abin da masu zunubi suke yi

ko zauna tare da masu yin ba’a.

Na neme ka da dukan zuciyata;

kada ka bar ni in kauce daga umarnanka.

Consequências

O Senhor recompensará cada um segundo suas obras. A justiça exalta a nação e traz segurança aos que a praticam.

Allah, "Zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikin da ya yi."

Ku tabbata cewa kada kowa rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi ƙoƙarin yin wa juna alheri da kuma dukan mutane.

Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. "Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita."

In kuma kana yin alheri ga masu yi maka ne kaɗai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma suna yin haka.

Tarko ne ga mutum ya keɓe wani abu da ba tunani

daga baya kuma ya yi la’akari da alkawarinsa.

Seja o primeiro

Este artigo te tocou? Faça uma oração!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.