Publicidade

Salmos 1

1 Mai farin ciki ne mutumin

da ba ya aiki da shawarar mugaye

ko yi abin da masu zunubi suke yi

ko zauna tare da masu yin ba’a.

2 Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji,

kuma yana ta nazarinta dare da rana.

3 Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa,

wanda yake ba da amfani a daidai lokaci

wanda kuma ganyensa ba sa bushewa.

Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.

4 Ba haka yake da mugaye ba!

Su kamar yayi ne

da iska take kwashewa.

5 Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba,

balle a sami masu zunubi a taron adalai.

6 Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa,

amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-