Pular para o conteúdo
Publicidade

Legalidades

Por Bíblia Online

A Bíblia reconhece a necessidade de leis e governo civil. Os cristãos são chamados a obedecer às autoridades estabelecidas por Deus, enquanto mantêm a lealdade suprema a Cristo.

Submissão às autoridades

Toda autoridade é instituída por Deus. O cristão é chamado a respeitar as leis, pagar tributos e honrar quem governa.

Biyayya ga masu mulki

Dole kowa yi biyayya ga masu mulki, gama babu wani iko sai ko in Allah ya yarda. Duk hukumomin da muke su, naɗin Allah ne. Saboda haka, duk wanda ya yi tawaye ga hukuma yana yin tawaye da abin da Allah ya naɗa ne, waɗanda kuwa suke aikata haka, za su jawo wa kansu hukunci. Gama masu mulki ba abin tsoro ba ne ga waɗanda suke yin abin da yake daidai, sai dai ga waɗanda suke aikata laifi. Kana so ka rabu da jin tsoron wanda yake mulki? To, sai ka aikata abin da yake daidai, zai kuwa yabe ka. Gama shi bawan Allah ne don kyautata rayuwarka. Amma in ka aikata mugunta, to, sai ka ji tsoro, don ba a banza ne shugaba yake ɗaukan takobinsa ba. Shi fa bawan Allah ne, ta wurinsa ne fushin Allah yakan hukunta masu laifi. Saboda haka, dole a yi biyayya ga hukumomi, ba don gudun horo kawai ba amma don lamirinku.

Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, gama hukumomin nan bayin Allah ne, waɗanda suke ba da dukan lokacinsu don aikin shugabanci. Ku ba wa kowa hakkinsa. In kuna da bashin haraji, sai ku biya; in kuɗin shiga ne, ku biya kuɗin shiga; in ladabi ne, ku yi ladabi; in kuma girmamawa ne, ku ba da girma.

Ku yi ƙauna, gama ranar ta yi kusa

Kada hakkin kowa zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan.

Ku yi irin rayuwa mai kyau a cikin masu bautar gumaka, yadda ko da sun zarge ku da yin laifi, za su iya ganin ayyukanku nagari, su ɗaukaka Allah a ranar da zai ziyarce mu.

Biyayya ga masu mulki da iyayengiji

Saboda Ubangiji, ku yi biyayya ga kowace hukumar da aka kafa cikin mutane, ko ga sarki, a matsayi wanda ya fi iko, ko ga gwamnoni, waɗanda ya aika domin su hukunta masu laifi su kuma yabi masu aikata abin da yake daidai.

To, ka gaya mana, a ra’ayinka? Ya dace a biya Kaisar haraji ko a’a?"

Amma Yesu da yake ya san mugun nufinsu, sai ya ce, "Ku munafukai, don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? Ku nuna mini kuɗin da ake biyan haraji da shi." Sai suka kawo masa dinari, sai ya tambaye su ya ce, "Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne?"

Suka amsa, "Na Kaisar ne."

Sai ya ce musu, "Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah."

Obrigações legais

Jesus cumpriu obrigações legais, pagou impostos e orientou seus seguidores a obedecer à lei sem comprometer a fé.

Harajin haikali

Bayan Yesu da almajiransa suka isa Kafarnahum, sai masu karɓan harajin rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, "Malaminku ba ya biyan harajin haikali ne?"

Ya amsa ya ce "I, yana biya."

Da Bitrus ya shiga gida, Yesu ne ya fara magana. Ya ce masa, "Me ka gani, Siman? Daga wurin wane ne sarakunan duniya suke karɓar kuɗin shiga da kuma haraji, daga wurin ya’yansu ne ko kuwa daga wurin waɗansu?"

Bitrus ya amsa ya ce, "Daga wurin waɗansu."

Yesu ya ce masa, "Wato, an ɗauke wa ya’yan ke nan. Amma don kada mu ɓata musu rai, ka je tafki ka jefa ƙugiyarka. Ka ɗauki kifin da ka fara kama; ka buɗe bakinsa, za ka sami shekel guda. Ka kawo ka ba su, harajina da naka ke nan."

"Ka yi hanzari ka shirya al’amura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku. Gaskiya nake gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.

Saboda ni, za a ja ku zuwa gaban gwamnoni da gaban sarakuna domin ku ba da shaida a gabansu, da kuma ga Al’ummai. Amma sa’ad da suka kama ku, kada ku damu game da abin da za ku faɗa ko kuwa yadda za ku faɗe shi. A lokacin za a ba ku abin da za ku faɗa,

Haihuwar Yesu

A waɗancan kwanaki, Kaisar Augustus ya ba da doka cewa ya kamata a yi ƙidaya a dukan masarautar Roma. (Wannan ce ƙidaya ta fari da aka yi a lokacin da Kwiriniyus yake gwamnar Suriya.) Sai kowa ya koma garinsa don a rubuta shi.

Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne. Ya tafi can don a rubuta shi tare da Maryamu, wadda aka yi masa alkawari zai aura, tana kuwa da ciki.

Perspectiva divina

As nações são como uma gota no balde diante de Deus. Ele abre portas que nenhuma lei pode fechar.

Tabbatacce al’ummai suna kama da ɗigon ruwa a cikin bokiti

an ɗauke su a matsayin ƙura a kan magwaji;

yakan auna tsibirai sai ka ce ƙura mai laushi.

A gabansa dukan al’ummai ba kome ba ne;

ya ɗauke su ba a bakin kome ba

kuma banza ne kurum.

domin an buɗe mini wata hanya mai fāɗi don aiki mai amfani, ko da yake akwai mutane da yawa masu gāba da ni.

Bilatus ya ce, "Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka san cewa ina da ikon sakinka, ko gicciye ka ba?"

Yesu ya amsa ya ce, "Ba ka da wani iko a kaina, in ba a ba ka daga sama ba. Saboda haka wanda ya bashe ni gare ka, ya fi na zunubi."

Seja o primeiro

Este artigo te tocou? Faça uma oração!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.