Pular para o conteúdo
Publicidade

Livro da vida

Por Bíblia Online

O Livro da Vida é o registro celestial dos nomes daqueles que pertencem a Deus. Estar escrito no Livro da Vida é a garantia da salvação eterna e da entrada na Nova Jerusalém.

Registrados no céu

Alegrai-vos por terem vossos nomes escritos nos céus. O Livro da Vida pertence ao Cordeiro de Deus desde a fundação do mundo.

Duk da haka, kada ku yi farin ciki da cewa, kun sha ƙarfin ruhohi, amma ku yi farin ciki, domin an rubuta sunayenku a sama."

I, ina kuma roƙonka, abokin famata, ka taimaki matan nan waɗanda suka yi fama aikin bishara tare da ni, haka ma Kilemen da kuma sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suna cikin littafin rai.

Dukan mazaunan duniya za su yi wa dabbar sujada, dukan waɗanda ba a rubuta sunayensu a cikin littafin ran da yake na Ɗan Ragon da aka yanka tun kafin halittar duniya ba.

Dabbar da ka gani, a ta taɓa kasancewa, a yanzu, ba ta, za kuma fito daga Abis zuwa ga hallakarta. Mazaunan duniya waɗanda ba a rubuta sunayensu a littafin rai tun kafin halittar duniya ba za su yi mamaki sa’ad da suka ga dabbar, domin a ta taɓa kasancewa, yanzu kuwa ba ta, duk da haka za dawo.

O juízo final

No dia do julgamento, os livros serão abertos. Quem não for encontrado no Livro da Vida será lançado no lago de fogo.

An shari’anta matattu

Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu. Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai. Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata. Sa’an nan aka jefar da mutuwa da kuma Hades cikin tafkin wuta. Tafkin wutar nan kuwa shi ne mutuwa ta biyu. Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan.

Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon.

Ƙarshe zamani

"A wannan lokaci Mika’ilu, babban mai mulki wanda yake kāre mutanenka, zai tashi. Za a yi lokacin matsananciyar wahala wanda ba a taɓa yi tun farkon ƙasashe har zuwa yanzu. Amma a lokacin da mutanenka, kowane mutum wanda aka sami sunansa a rubuce a cikin littafin, za a cece shi. Ɗumbun mutanen da suka yi barci cikin turɓayar duniya za su farka, waɗansu zuwa ga rai madawwami, waɗansu zuwa ga madawwamiyar kunya da kuma madawwamin ƙasƙanci.

Wanda ya ci nasara, kamar su, za a sanya masa fararen tufafi. Ba zan taɓa share sunansa daga cikin littafin rai ba, sai dai zan shaida sunansa a gaban Ubana da mala’ikunsa.

O registro divino

Deus registra cada vida, cada lágrima e cada momento. Nada passa despercebido diante daquele que tudo vê e tudo guarda.

Idanunka sun ga jikina marar fasali;

dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka

kafin ɗayansu kasance.

Ka lissafta makokina;

ka jera hawayena a littafinka,

ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?

Gama sun tsananta wa waɗanda ka hukunta

suna kuma taɗin wahalar waɗanda ka ji musu rauni.

Ka neme su da laifi a kan laifi;

kada ka bar su su sami rabo a cikin cetonka.

Bari a shafe su sarai daga littafin rai

kada a kuma lissafta su tare da adalai.

Sa’an nan waɗanda suke tsoron Ubangiji suka yi magana da juna, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya kuma ji. A gabansa aka rubuta a littafin tarihi waɗanda suke tsoron Ubangiji, suna kuma girmama sunansa.

Amma yanzu, ina roƙonka ka gafarta zunubinsu, in ba haka ba, to, ka shafe ni daga littafin da ka rubuta."

Ubangiji ya amsa wa Musa, "Duk wanda ya yi mini zunubi, shi zan shafe daga littafina.

Seja o primeiro

Este artigo te tocou? Faça uma oração!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.