Meditação
A meditação na Palavra de Deus é prática espiritual essencial. Diferente da meditação oriental, a meditação bíblica é reflexão profunda sobre as Escrituras — ruminar a Palavra dia e noite.
Meditar na Palavra dia e noite
Bem-aventurado o homem que medita na lei do Senhor de dia e de noite. Ele é como árvore plantada junto a ribeiros de águas.
Mai farin ciki ne mutumin
da ba ya aiki da shawarar mugaye
ko yă yi abin da masu zunubi suke yi
ko yă zauna tare da masu yin ba’a.
Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji,
kuma yana ta nazarinta dare da rana.
Kada ka bar Littafin Dokokin nan yă rabu da bakinka, sai dai ka yi ta tunani game da shi dare da rana, don ka lura, ka yi duk abin da aka rubuta a ciki, ta haka ne za ka yi nasara cikin duk abin da za ka yi.
Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka!
Ina tunani a kanta dukan yini.
Umarnanka suna sa in zama mai hikima fiye da abokan gābana,
gama kullum suna tare da ni.
Ina da ganewa sosai fiye da dukan malamaina,
gama ina tunani a kan farillanka.
Ina da ganewa fiye da dattawa,
gama ina biyayya da farillanka.
Na yi tunani a kan farillanka
na kuma lura da hanyoyinka.
Na yi murna a cikin ƙa’idodinka;
ba zan ƙyale maganarka ba.
ג Gimel
gama ina farin ciki da umarnanka
saboda ina ƙaunarsu.
Na ɗaga hannuwana ga umarnanka, waɗanda nake ƙauna,
ina kuma tunani a kan ƙa’idodinka.
ז Zayin
Na tashi kafin fitowar rana na kuma yi kukan neman taimako;
na sa zuciyata a maganarka.
Ban rufe idanuna ba dukan dare,
don in yi tunani a kan alkawuranka.
Frutos da meditação
A meditação produz entendimento, alegria e adoração. Quem medita na Palavra encontra direção, paz e renovação espiritual.
Bari kalmomin bakina da tunanin zuciyata
su zama abin gamsuwa a gabanka,
Ya Ubangiji, Dutsena da Mai fansata.
Bakina zai yi maganar hikima;
magana daga zuciyata za tă ba da ganewa.
Zan tuna da ayyukan Ubangiji;
I, zan tuna mu’ujizanka na tun dā.
Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka
in lura da dukan manyan abubuwan da ka aikata.
Na tuna da kwanakin baya
na yi tunani a kan dukan ayyukanka
na kuma lura da abin da hannuwanka suka yi.
Cikin haikalinka, ya Allah,
mun yi tunani a kan ƙaunarka marar ƙarewa.
Zan rera ga Ubangiji dukan raina;
zan rera yabo ga Allahna muddin ina raye.
Bari tunanina yă gamshe shi,
yayinda nake farin ciki a cikin Ubangiji.