Publicidade

Misericórdia

Por Bíblia Online

A misericórdia de Deus é eterna e inesgotável. Ele se compadece dos que sofrem, perdoa os arrependidos e derrama graça sobre os que não merecem. Grande é a sua fidelidade.

A misericórdia de Deus

Quem é Deus como tu, que perdoa a iniquidade? Ele se deleita em ter misericórdia e não retém a ira para sempre.

Wane ne Allah kamar ka,

wanda yake yafe zunubi yă kuma gafarta laifofin mutanensa da suka ragu?

Ba ka zama mai fushi har abada

amma kana marmari ka nuna jinƙai.

Ka yi mini jinƙai, ya Allah,

bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa;

bisa ga tausayinka mai girma

ka shafe laifofina.

Ka wanke dukan kurakuraina

ka tsarkake ni daga zunubina.

Ka tuna, ya Ubangiji da jinƙai da kuma ƙaunarka mai girma,

gama suna nan tun dā.

Kada ka tuna da zunuban ƙuruciyata

da kuma hanyoyin tawayena;

bisa ga ƙaunarka ka tuna da ni,

gama kai nagari ne, ya Ubangiji.

Daga cikin zurfafa na yi kuka gare ka, ya Ubangiji;

Ya Ubangiji, ka ji muryata.

Bari kunnuwanka su saurara

ga kukata ta neman jinƙai.

Kada ka hana mini jinƙanka, ya Ubangiji;

bari ƙaunarka da gaskiyarka kullum su kāre ni.

Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi

dukan kwanakin raina,

zan kuwa zauna a gidan Ubangiji

har abada.

Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa,

haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa;

Graça e perdão

Onde o pecado abundou, superabundou a graça. Deus convida todos ao arrependimento e promete perdão total aos que confessam.

Amma kyautan nan dabam take da laifin nan. Gama in mutane da yawa sun mutu saboda laifin mutum ɗayan nan, to, ai, alherin Allah da kuma kyautan nan mai zuwa ta wurin alherin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi, ya shafi mutane da yawa!

Me za mu ce ke nan? Za mu ci gaba yin zunubi domin ba ma ƙarƙashin doka sai dai ƙarƙashin alheri? Sam, ko kaɗan!

Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai, ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku.

Amma ya ce mini, "Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona." Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni.

Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara,

amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai.

Bari mugu ya bar irin halinsa

mugu kuma ya sāke irin tunaninsa.

Bari yă juyo ga Ubangiji, zai kuwa ji tausayinsa,

ya juyo ga Allahnmu kuma, gama shi mai gafartawa ne a sauƙaƙe.

Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri;

ya tashi don yă nuna muku jinƙai.

Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya.

Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!

Misericórdia e compaixão

Misericórdia quero e não sacrifício. Deus nos chama a ser misericordiosos como Ele é, perdoando e acolhendo o próximo.

Amma ku je ku koyi abin da wannan yake nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba.’ Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi."

Sai Bitrus ya zo wurin Yesu ya yi masa tambaya ya ce, "Ubangiji, sau nawa zan yafe wa ɗan’uwana sa’ad da ya yi mini zunubi? Har sau bakwai?"

Yesu amsa ya ce, "Ina gaya maka, ba sau bakwai ba, amma sau saba’in da bakwai.

Gama in kuna yafe wa mutane sa’ad da suka yi muku laifi, Ubanku da yake cikin sama ma zai gafarta muku.

Amma cikin tausayinka mai girma ba ka kawo su ga ƙarshe ko ka yashe su ba, gama kai Allah ne mai alheri da kuma mai jinƙai.

Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake,

shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya.

Bari alherin shugabanmu Allah yă kasance a kanmu;

ka albarkaci mana aikin hannuwanmu,

I, ka albarkaci aikin hannuwanmu.

Acessar a misericórdia

Cheguemos com confiança ao trono da graça. Ali encontramos misericórdia e graça para socorro no tempo oportuno.

Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.

Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya.

Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami.

Gama an ba ku zarafi a madadin Kiristi cewa ba gaskatawa da shi kaɗai ba kuka yi ba, har ma ku sha wahala dominsa,

Hezekiya ya yi Bikin Ƙetarewa

Sai Hezekiya ya aika wa dukan Isra’ila da Yahuda, ya kuma rubuta wasiƙu zuwa Efraim da Manasse, yana gayyatarsu su zo haikalin Ubangiji a Urushalima, su kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji, Allah na Isra’ila. Sarki da fadawansa da dukan taro a Urushalima suka yanke shawara su yi Bikin Ƙetarewa a wata na biyu. Ba su iya yinsa a daidai lokacinsa ba domin babu isashen firistocin da suka tsarkake kansu, mutane kuma ba su taru a Urushalima ba. Shirin ya yi kyau ga sarki da kuma dukan taron. Suka yanke shawara su yi shelar a ko’ina a Isra’ila, daga Beyersheba zuwa Dan, suna kiran mutane su zo Urushalima, suka kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allah na Isra’ila. Ba a yi bikin da mutane masu yawa bisa ga abin da aka rubuta ba.

Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan aika suka tafi ko’ina a Isra’ila da Yahuda da wasiƙu daga sarki da kuma daga fadawansa, wasiƙar tana cewa,

"Mutanen Isra’ila, ku dawo ga Ubangiji Allah na Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, domin yă dawo gare ku, ku da kuka tafi, ku da kuka kuɓuce daga hannun sarakuna Assuriya. Kada ku zama kamar iyayenku da ’yan’uwanku, waɗanda suka yi rashin aminci ga Ubangiji Allah na kakanninsu, har ya mai da su abin tsoro, yadda kuke gani. Kada ku yi taurinkai, yadda iyayenku suka yi; ku miƙa kai ga Ubangiji. Ku zo wuri mai tsarki, wanda ya tsarkake har abada. Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin fushi mai zafi yă juye daga gare ku. In kuka dawo wurin Ubangiji, sa’an nan waɗanda suka kama ’yan’uwanku da ’ya’yanku za su nuna musu tausayi, su kuma dawo wannan ƙasa, gama Ubangiji Allahnku mai alheri ne mai jinƙai kuma. Ba zai kau da fuskarsa daga gare ku ba, in kuka dawo gare shi."

’Yan aika suka tafi gari-gari a cikin Efraim da Manasse, har zuwa Zebulun, amma mutane suka yi musu dariyar reni, suka kuma yi musu ba’a. Duk da haka, waɗansu mutanen Asher, Manasse da Zebulun suka ƙasƙantar da kansu suka tafi Urushalima. Haka ma a Yahuda, hannun Allah yana a kan mutane don yă ba su zuciya ɗaya su yi abin da sarki da fadawansa suka umarta, suna bin maganar Ubangiji.

Taron mutane mai girma ya haɗu a Urushalima don Bikin Burodi Marar Yisti a wata na biyu. Suka kawar da bagadai a Urushalima suka fid da bagadan turare suka zubar da su a Kwarin Kidron.

Suka yanka ɗan ragon Bikin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu na wata na biyu. Firistoci da Lawiyawa suka ji kunya suka tsarkake kansu, suka kawo hadayun ƙonawa a haikalin Ubangiji. Sa’an nan suka ɗauki matsayinsu na kullum yadda yake a Dokar Musa mutumin Allah. Firistoci suka yayyafa jinin da Lawiyawa suka ba su. Da yake da yawa cikin taron ba su tsarkake kansu ba, dole Lawiyawa su yanka ’yan ragunan Bikin Ƙetarewa domin dukan waɗanda ba su da tsarki, ba su kuma iya tsarkake ragunansu ga Ubangiji ba. Ko da yake yawancin mutanen da suka zo daga Efraim, Manasse, Issakar da Zebulun ba su tsarkake kansu ba, duk da haka suka ci Bikin Ƙetarewa, ba tare da bin abin da yake a rubuce ba. Amma Hezekiya ya yi addu’a dominsu cewa, "Bari Ubangiji, wanda yake nagari, yă gafarta wa kowa wanda ya sa zuciyarsa ga neman Allah, Ubangiji Allah na kakanninsa, ko da shi marar tsarki ne bisa ga dokokin wuri mai tsarki." Ubangiji kuwa ya ji Hezekiya ya kuma warkar da mutane.

Isra’ilawan da suka kasance a Urushalima suka yi Bikin Burodi Marar Yisti kwana bakwai da farin ciki mai girma, yayinda Lawiyawa da firistoci suke rera ga Ubangiji kowace rana, haɗe da kayan kiɗin yabon Ubangiji.

Hezekiya ya yi magana mai ƙarfafawa ga dukan Lawiyawa waɗanda suka nuna ganewar fasaha a hidimar Ubangiji. Kwana bakwai suka ci rabonsu da aka tsara, suka miƙa hadayun salama, suka kuma yabi Ubangiji Allah na kakanninsu.

Dukan mutanen suka yarda su ƙara kwana bakwai kuma, sai suka ci gaba da bikin cikin farin ciki har waɗansu kwana bakwai kuma. Hezekiya sarkin Yahuda ya tanada bijimai dubu ɗaya da tumaki da kuma awaki dubu bakwai wa taron, fadawa kuma suka tanada musu bijimai dubu da kuma tumaki da awaki dubu goma. Firistoci masu yawa suka tsarkake kansu. Taron gaba ɗaya na Yahuda suka yi farin ciki, tare da firistoci da kuma Lawiyawa da dukan waɗanda suka taru daga Isra’ila, har ma da baƙi waɗanda suka zo daga Isra’ila da waɗanda suke zama a Yahuda. Aka yi farin ciki mai girma a Urushalima, gama tun zamanin Solomon ɗan Dawuda sarkin Isra’ila, ba a taɓa yin wani abu kamar haka a Urushalima ba. Firistoci da Lawiyawa suka tsaya suka albarkace mutane, Allah kuma ya ji su, gama addu’arsu ya kai sama, mazauninsa mai tsarki.

"In mutum ya saki matarsa

ta kuwa bar shi ta auri wani mutum,

zai iya komo da ita kuma?

Ƙasar ba za tă ƙazantu gaba ɗaya ba?

Amma kun yi rayuwa kamar karuwa da masoya masu yawa

yanzu za ki komo wurina?"

In ji Ubangiji.

"Ta da idanu ki duba tsaunuka ki gani.

Akwai wani wurin da ba a kwana da ke ba?

A gefen hanya kin zauna kina jiran masoyanki,

kin zauna kamar makiyayi a hamada.

Kin ƙazantar da ƙasar

da karuwancinki da muguntarki.

Saboda haka an hana yayyafi,

kuma babu ruwan bazara da ya sauka.

Duk da haka kina da irin kallon da karuwa takan yi;

kin ƙi ki ji kunya.

Yanzu ba kin kira ni,

‘Mahaifina, abokina daga ƙuruciyata ba,

kullum za ka riƙa fushi?

Hasalarka za tă ci gaba har abada ne?’

Haka kike magana,

amma kina aikata dukan muguntar da kika iya yi."

Isra’ila marar aminci

A zamanin Sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, "Ka ga abin da marar amincin nan, Isra’ila ta yi? Ta haura kan kowane tudu mai tsayi da kowane gindin itace mai duhuwa ta yi zina a can. Na yi zaton bayan ta yi wannan duka, za tă komo wurina amma ba tă yi haka ba, ’yar’uwarta marar aminci nan Yahuda ta gani. Na ba wa Isra’ila marar bangaskiya takardar saki na kuwa kore ta saboda duk zinanta. Duk da haka na ga cewa ’yar’uwarta marar amincin nan Yahuda ba ta da tsoro; ita ma ta fita ta yi zina. Domin fasikancin Isra’ila bai yi tasiri gare ta ba, sai ta ƙazantar da ƙasar ta kuma yi zina da dutse da kuma itace. Duk da wannan duka, Yahuda ’yar’uwarta rashin amincin ba tă komo gare ni da dukan zuciyarta ba, sai a munafunce," in ji Ubangiji.

Ubangiji ya ce mini, "Isra’ila marar bangaskiya ta fi Yahuda marar aminci. Ka tafi, ka yi shelar saƙon nan wajen arewa cewa,

" ‘Ki komo, Isra’ila marar bangaskiya,’ in ji Ubangiji,

‘Ba zan ƙara yin fushi da ke ba,

gama ni mai jinƙai ne,’ in ji Ubangiji,

‘Ba zan yi fushi da ke har abada ba.

Ki dai yarda da laifinki

kin yi wa Ubangiji Allahnki tawaye,

kin watsar da alheranki ga baƙin alloli

a ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa,

ba ki kuwa yi mini biyayya ba,’ "

in ji Ubangiji.

"Ku komo, ku mutane marasa bangaskiya," in ji Ubangiji, "gama ni ne mijinku. Zan ɗauke ku, ɗaya daga garuruwanku da kuma biyu daga zuriyarku in kawo ku a Sihiyona. Sa’an nan zan ba ku makiyaya da suke yin abin da zuciyata take so, waɗanda za su bishe ku da sani da kuma fahimi. A kwanakin, sa’ad da kuka ƙaru sosai a ƙasar," in ji Ubangiji, "mutane ba za su ƙara yin magana a kan, ‘Akwatin alkawarin Ubangiji ba.’ Ba zai ƙara shiga zuciyarsu ko su tuna ba; ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba. A lokacin za su ce da Urushalima Kursiyin Ubangiji, kuma dukan al’ummai za su taru a Urushalima don su girmama sunan Ubangiji. Ba za su ƙara bin taurinkai zuciyarsu mai mugunta ba. A kwanakin gidan Yahuda zai haɗu da gidan Isra’ila, tare kuma za su zo daga ƙasar da take wajen arewa zuwa ƙasar da na ba kakanninsu gādo.

"Ni kaina na faɗa,

" ‘Da farin ciki zan ɗauke ki kamar ’ya’yana maza

in ba ki ƙasa mai daɗi,

gādo mafi kyau da wata al’umma.’

Na zaci za ki kira ni ‘Mahaifi’

ba za ki ƙara rabuwa da bina ba.

Amma kamar mace marar aminci ga mijinta,

haka kika kasance marar aminci gare ni, ya gidan Isra’ila,"

in ji Ubangiji.

An ji kuka a filayen tuddai,

kuka da roƙon mutanen Isra’ila,

domin sun lalace hanyoyinsu

sun kuma manta da Ubangiji Allahnsu.

"Ku komo, mutane marasa bangaskiya;

zan warkar da ku daga ja da bayanku."

"I, za mu zo wurinka,

gama kai ne Ubangiji Allahnmu.

Tabbatacce hayaniyar bin gumaka a kan tuddai

da duwatsu banza ne;

tabbatacce a wurin Ubangiji Allahnmu ne

akwai ceton Isra’ila.

Daga ƙuruciyarmu allolin kunya sun cinye mu

amfanin wahalar kakanninmu

garkunan tumakinsu da na awakinsu,

yaransu maza da mata.

Bari mu kwanta mu sha kunya,

bari kuma kunyarmu ta rufe mu.

Mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi,

da mu da kakanninmu;

daga ƙuruciyarmu har yă zuwa yau

ba mu yi wa Ubangiji Allahnmu biyayya ba."

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-20_17-16-08-