Pular para o conteúdo
Publicidade

Farawa 49

Yaƙub ya albarkaci ya’yansa maza

1 Sai Yaƙub ya kira ya’yansa maza ya ce, "Ku tattaru don in faɗa muku abin da zai faru gare ku, a kwanaki masu zuwa.

2 "Ku tattaru, ku saurara, ya’yan Yaƙub maza;

ku saurari mahaifinku, Isra’ila.

3 "Ruben, kai ne ɗan farina,

ƙarfina, alamar farko ta ƙarfina,

mafi matsayi, kuma mafi iko.

4 Mai tumbatsa kamar ruwa, amma ba za ka ƙara zama mai daraja ba,

gama ka hau gadon mahaifinka

ka hau kujerata, ka kuma ƙazantar da shi.

5 "Simeyon da Lawi yan’uwa ne,

takubansu makamai ne na da hankali.

6 Ba zan shiga shawararsu ba,

ba zan shiga taronsu ba,

gama sun kashe maza cikin fushinsu

cikin ganin dama suka kashe bijimai.

7 La’ananne ne fushinsu, mai tsanani ne ƙwarai,

hasalarsu kuwa, muguwa ce ƙwarai!

Zan warwatsa su cikin Yaƙub

in kuma daidaita su cikin Isra’ila.

8 "Yahuda,49.8 Yahuda ya yi kamar ya fito daga Ibraniyanci na yabo ne. yan’uwanka za su yabe ka;

hannuwanka za su kasance a wuyan abokan gābanka,

ya’yan mahaifinka maza za su rusuna maka.

9 Kai ɗan zaki ne, ya Yahuda,

ka dawo daga farauta, ɗana.

Kamar zaki, yakan kwanta a miƙe,

kamar zakanya, wa yake da ƙarfin halin tashe shi?

10 Kursiyi ba zai tashi daga Yahuda ba,

ba kuwa sandan mulki daga tsakani ƙafafunsa ba,

sai ya zo ga wanda yake mai shi49.10 Ko kuwa sai Shilo ya zo; ko kuwa sai ya zo ga girma ya dace..

Biyayyar al’umma kuwa tasa ce.

11 Zai daure jakinsa a kuringa,

aholakinsa a rassa mafi kyau;

zai wanke tufafinsa cikin ruwan inabi

rigunansa cikin inabi ja wur kamar jini.

12 Idanunsa za su duhunce fiye da ruwan inabi,

haƙorarsa farare kamar madara.49.12 Ko kuwa zai zama marar walƙiya daga ruwan inabi, haƙorarsa farare daga madara

13 "Zebulun zai zauna a bakin teku,

zama tasar jiragen ruwa;

iyakarsa za nausa zuwa Sidon.

14 "Issakar doki49.14 Ko kuwa mai ƙarfi mai ƙarfi,

kwance tsakanin buhunan sirdi.49.14 Ko kuwa sansanin wuta

15 Sa’ad da ya ga yadda wurin hutunsa yana da kyau

da kuma daɗin da ƙasarsa take,

zan tanƙware kafaɗarsa ga nauyi

miƙa kai ga aikin dole.

16 "Dan49.16 Dan a nan yana nufin yakan tanada adalci. zai tanada adalci wa mutanensa

kamar ɗaya cikin kabilan Isra’ila.

17 Dan zai zama maciji a gefen hanya,

kububuwa a bakin hanya,

da take saran ɗiɗɗigen doki

domin mahayinsa fāɗi da baya.

18 "Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji.

19 "Masu fashi za su fāɗa wa Gad,49.19 Gad na iya nufin fāɗawa da kuma ƙungiyar mahara.

amma zai runtume su.

20 "Abincin Asher zai zama a wadace,

zai yi tanadin abinci iri-iri da suka dace don sarki.

21 "Naftali sakakkiyar barewa ce

da take haihuwar kyawawan ya’ya.49.21 Ko kuwa yakan faɗa kyawawan kalmomi

22 "Yusuf kuringa ce mai ba da amfani.

Kuringa mai ba da amfani kusa da rafi

wadda rassanta na hawan bango.49.22 Ko kuwa Yusuf aholakin jeji ne, aholakin jeji kusa da rafi, jakin jeji a tudun mai kunyoyi

23 Da ɗaci rai mahara suka fāɗa masa;

suka harbe shi babu tausayi.

24 Amma bakansa yana nan daram

hannuwansa masu ƙarfi ba sa jijjiguwa49.23,24 Ko kuwa mahara za su fāɗa, za su harba, za su rage, za su tsaya

saboda hannun Maɗaukaki na Yaƙub,

saboda Makiyayi, Dutsen Isra’ila,

25 saboda Allah na mahaifinka, wanda ya taimake ka,

saboda Maɗaukaki,49.25 Da Ibraniyanci Shaddai wanda yake albarkace ka

da albarkar sama da take bisa

albarkun zurfafa da suke ƙarƙashin ƙasa

albarkun mama da kuma mahaifa.

26 Albarkun mahaifi suna da girma fiye

da albarkun daɗaɗɗun duwatsu

fiye49.26 Ko kuwa kakana, mai girma kamar da yalwar madawwaman tuddai.

Bari dukan waɗannan su zauna a kan Yusuf,

a goshin ɗan sarki a cikin49.26 Ko kuwa wanda aka raba da yan’uwansa.

27 "Benyamin kyarkeci ne mai kisa;

da safe yakan cinye abin da ya farauto

da yamma yakan raba ganima."

28 Dukan waɗannan su ne kabilu goma sha biyu na Isra’ila, kuma abin da mahaifinsu ya faɗa musu ke nan sa’ad da ya albarkace su, yana ba kowane albarkar da ta dace da shi.

Mutuwar Yaƙub

29 Sa’an nan ya ba su waɗannan umarnai ya ce, "Ina gab da a tara ni ga mutanena. Ku binne ni tare da kakannina a kogon da yake cikin filin Efron mutumin Hitti, 30 kogon da yake cikin filin Makfela, kusa da Mamre a Kan’ana, wanda Ibrahim ya saya tare da filin, zama makabarta daga Efron mutumin Hitti. 31 A can aka binne Ibrahim da matarsa Saratu, a can aka binne Ishaku da matarsa Rebeka, a can kuma na binne Liyatu. 32 Filin tare da kogon da yake ciki, an saya daga Hittiyawa."49.32 Ko kuwa ’ya’ya mazan Het

33 Sa’ad da Yaƙub ya gama ba da umarnan ga ya’yansa maza, sai ya ɗaga ƙafafunsa zuwa gado, ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa tara shi ga mutanensa.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também