Motivação
Motivação verdadeira vem de Deus. A Bíblia nos inspira a correr a carreira da fé com perseverança, sabendo que o Senhor fortalece, guia e recompensa os fiéis.
Força do alto
Tudo posso naquele que me fortalece. Deus dá poder aos fracos e renova a força dos cansados — Ele é a fonte de toda motivação.
Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.
Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji
yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.
Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,
samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;
amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji
za su sabunta ƙarfinsu.
Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;
za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,
za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji;
raina yana farin ciki a cikin Allahna.
Gama ya suturce ni da rigunan ceto
ya yi mini ado da rigar adalci,
yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist
kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja.
gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau.
Correr para o alvo
Prossigo para o alvo, para o prêmio da soberana vocação de Deus em Cristo Jesus. A corrida da fé exige disciplina e foco.
’Yan’uwa, ban ɗauki kaina a kan cewa na riga na sami abin ba. Sai dai abu guda nake yi. Ina mantawa da abin da yake baya, ina kuma nacewa zuwa ga samun abin da yake gaba, ina nacewa gaba zuwa ga manufar, don in sami ladar da Allah ya yi mini na kiran nan zuwa sama a cikin Kiristi Yesu.
Ba ku sani ba cewa a gasar gudu, dukan masu gudu sukan yi gudu, amma guda ne kaɗai yakan sami lada? To, sai ku yi gudu yadda za ku sami lada. Duk ’yan wasan gasa sukan hori kansu sosai. Sukan yi haka domin su sami rawanin da ba zai daɗe ba. Amma mu muna yi ne domin mu sami rawanin da zai dawwama. To, ni fa ba gudu nake yi kamar mai gudu ba wurin zuwa ba. Dambena kuma ba naushin iska nake yi ba. A’a, ina horon jikina in mai da shi bawana, saboda bayan na yi wa waɗansu wa’azi, ni kaina kada in kāsa cancantar samun lada.
Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa. Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah. Ku lura da wannan wanda ya jure da irin hamayyan nan daga masu zunubi, don kada ku gaji, har ku fid da zuciya.
Kome kuke yi, ku yi shi da dukan zuciyarku, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba ga mutum ba.
Propósito e missão
Deus tem planos de esperança para nós. Cada dia é oportunidade de fazer a sua vontade e avançar com confiança na missão.
Gama na san shirye-shiryen da na yi muku," in ji Ubangiji, "shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.
Kuma zan yi duk abin da kuka roƙa cikin sunana, don Ɗan ya kawo ɗaukaka ga Uban. Za ku iya roƙe ni kome a cikin sunana, zan kuwa yi.
Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin da Gal 3.27 sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki, kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani."
Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba."
Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima.
Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka,
dubu goma a hannun damanka,
amma ba abin da zai zo kusa da kai.
Kada ku sa zuciyarku a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada ku damu a kan su. Gama duniya da ba tă san Allah ba, tana faman neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa, ya san kuna bukatarsu.
Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, "In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci."
Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum. Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci. Game da ku kuma ’yan’uwa, kada ku gaji da yin abin da yake daidai.