Mundo
A Bíblia tem muito a dizer sobre o mundo e nossa relação com ele. Cristãos estão no mundo, mas não são do mundo — chamados a ser luz e sal sem se conformar com os padrões seculares.
Não ameis o mundo
Não ameis o mundo nem o que nele há. A cobiça da carne, a cobiça dos olhos e a soberba da vida não vêm do Pai, mas do mundo.
Kada ku ƙaunaci duniya
Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa.
Kada ku ƙaunaci duniya
Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa. Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya.
Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya.
Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada.
Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yă zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan.
Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yă zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan.
O amor de Deus pelo mundo
Porque Deus amou o mundo de tal maneira que deu seu Filho. O mesmo mundo que rejeita a Deus é amado por Ele e objeto de sua redenção.
Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami.
Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami.
Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne.
Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka.
Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba.
Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba.
Vencer o mundo
Jesus venceu o mundo e nos dá sua paz e vitória. A fé é a vitória que vence o mundo — e aquele que nasceu de Deus o vence.
"Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya."
"Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya."
domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya.
domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya.
Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne.
Ku, ’ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma.
No mundo sem ser do mundo
Jesus orou: não peço que os tires do mundo, mas que os guardes do mal. Somos enviados ao mundo como embaixadores do Reino.
Na gaya musu maganarka duniya kuwa ta ƙi su, don su ba na duniya ba ne yadda ni ma ba na duniya ba ne.
Ba addu’ata ba ce ka ɗauke su daga duniya ba, sai dai ka kāre su daga mugun nan.
Ba addu’ata ba ce ka ɗauke su daga duniya ba, sai dai ka kāre su daga mugun nan. Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya. Kamar yadda ka aiko ni cikin duniya, haka ni ma na aike su cikin duniya.
"Ya Uba Mai Adalci, ko da yake duniya ba tă san ka ba, ni na san ka, sun kuma san kai ka aiko ni. Na bayyana ka a gare su, zan kuma ci gaba da bayyana ka domin ƙaunar da ka yi mini ta kasance a cikinsu ni ma in kasance a cikinsu."
Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shari’a, yanzu ne za a tumɓuke mai mulkin duniyan nan.
Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.
Duniya ta ƙi jinin almajirai
"In duniya ta ƙi ku, ku san cewa ta fara ƙin na ne. Da ku na duniya ne, da ta ƙaunaci abinta. Kamar yadda yake, ku ba na duniya ba ne, na zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku.
Sal e luz
Vós sois o sal da terra e a luz do mundo. O cristão transforma o ambiente onde está, sem se conformar com os padrões mundanos.
Gishiri da kuma haske
"Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka.
"Ku ne hasken duniya. Birnin da yake a bisan tudu ba ya ɓoyuwa.
Za a kuma yi wa’azin wannan bisharar mulki a cikin dukan duniya, yă zama shaida ga dukan al’ummai, sa’an nan ƙarshen yă zo.
Me mutum zai amfana in ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai bayar a bakin ransa?
Me mutum zai amfana in ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai bayar a bakin ransa?
Kaiton duniya saboda abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi! Dole irin waɗannan abubuwa su zo, sai dai kaiton mutumin da ya zama sanadin kawo su!
Ya ce, musu, "Ku tafi cikin dukan duniya, ku yi wa’azin bishara ga dukan halitta.
Ya ce, musu, "Ku tafi cikin dukan duniya, ku yi wa’azin bishara ga dukan halitta.
Me mutum zai amfana, in ya ribato duniya duka a bakin ransa?
Não se conformar
Não vos conformeis com este mundo. A religião pura é guardar-se da corrupção do mundo e viver segundo o Espírito de Deus.
Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.
Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.
Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.
Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.
Yanzu mun san cewa dukan abin da doka ta ce, tana magana ne ga waɗanda suke ƙarƙarshin doka, saboda a rufe kowane baki; dukan duniya kuma ta ba da lissafin kanta a gaban Allah.
Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.
Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.
Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane. Yana koya mana mu ce, "A’a" ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani,
A batalha espiritual
A nossa luta não é contra carne e sangue. Os poderes do mundo são reais, mas o que está em nós é maior que o que está no mundo.
Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama.
Ku lura kada wani yă ruɗe ku da ilimin banza da wofi. Wannan koyarwa ta mutane ce kawai. Ta fito daga ikokin wannan duniya ne ba daga Kiristi ba.
Ko da yake muna cikin duniya, ba ma yaƙi kamar yadda duniya take yi.
Ba mu karɓi ruhun duniya ba, sai dai Ruhun da yake daga Allah, domin mu fahimci abin da Allah ya ba mu hannu sake.
Ina mai hikima? Ina mai zurfin bincike? Ina masana na wannan zamani? Ashe, Allah bai wofinta hikimar duniya ba? Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba tă san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar wa’azin bishara.
Amma Allah ya zaɓi abubuwa masu wautata duniya, don yă kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abubuwa marasa ƙarfi na duniya, domin ya ba wa masu ƙarfi kunya.
Ya zaɓi abubuwa marasa martaba na wannan duniya da kuma abubuwan da aka rena da abubuwan da ba a ɗauka a bakin kome ba, domin a wofinta abubuwan da ake ganinsu da daraja, domin kada wani ya yi taƙama a gabansa.
Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa "wawa" don yă zama mai hikima.
Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba. In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su.
Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba. In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su.
Pertencemos a Deus
Do Senhor é a terra e tudo o que nela existe. Vivemos neste mundo como peregrinos, desejando a pátria celestial.
Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta,
duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta;
gama ya gina ta a kan tekuna
ya kafa ta a kan ruwaye.
Sammai naka ne, haka kuma duniya;
ka kafa duniya da dukan abin da yake cikinta.
Alherinka da girma yake,
wanda ka ajiye domin waɗanda suke tsoronka,
wanda ka mayar a gaban mutane
a kan waɗanda suke neman mafaka daga gare ka.
Ubangiji yana mulki har abada;
ya kafa kujerarsa don shari’a.
Zai hukunta duniya da adalci;
zai yi mulkin mutane cikin gaskiya.
Haske na gaskiya da yake ba da haske ga kowane mutum mai shigowa duniya. Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba tă gane shi ba.
Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba tă gane shi ba.
Gaskiyar shaidar Yesu
Sa’ad da Yesu ya sāke magana da mutanen, sai ya ce, "Ni ne hasken duniya. Duk wanda ya bi ni ba zai yi tafiya cikin duhu ba, sai dai yă sami hasken rayuwa."
Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na. Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.
Amma gaskiya nake gaya muku. Don amfaninku ne zan tafi. Sai ko na tafi, in ba haka ba Mai Taimakon nan ba zai zo muku ba. Amma in na tafi, zan aiko shi gare ku. Sa’ad da ya zo kuwa, zai kā da duniya a kan zunubi da adalci da kuma hukunci, a kan zunubi, domin mutane ba su gaskata da ni ba; a kan adalci, domin zan tafi wurin Uba, inda ba za ku ƙara ganina ba; a kan hukunci kuma, domin an yanke hukunci a kan mai mulkin duniyan nan.
Ta wurin waɗannan ya ba mu alkawaransa masu girma da kuma masu daraja, domin ta wurinsu ku iya yin tarayya cikin Allahntakarsa, ku kuma kuɓuta daga lalatar da take cikin duniya wadda mugayen sha’awace-sha’awace suke jawowa.
Da farko dai, dole ku fahimci wannan cewa a kwanakin ƙarshe masu ba’a za su zo suna ba’a, suna bin mugayen sha’awace-sha’awacensu. Za su ce, "Ina wannan ‘dawowar’ da ya yi alkawari ne? Tun mutuwar kakanninmu, kome yana tafiya kamar yadda yake tun farkon halitta." Amma da gangan suke manta cewa tun dā can ta wurin maganar Allah sammai suka kasance aka kuma yi ƙasa daga ruwa ta wurin ruwa kuma. Ta wurin waɗannan ruwan ne aka nutsar, aka kuma hallakar da duniya ta wancan lokaci. Ta wurin wannan magana ce aka ajiye sammai da ƙasa na yanzu domin wuta, an ajiye su kuma don ranar hukunci da hallaka ta mutane marasa tsoron Allah.
Baƙin ciki irin na tsoron Allah yana kai ga tuban da yake kawo ceto, ba ya kuma kawo baƙin ciki, amma baƙin ciki irin na duniya yakan kawo mutuwa.
Zan hukunta duniya saboda muguntarta,
mugaye saboda zunubansu.
Zan kawo ƙarshe ga girman kan masu taƙama
in kuma ƙasƙantar da ɗaga kan marasa tausayi.
Kada ku yi mamaki ’yan’uwana, in duniya ta ƙi ku.
Mun san cewa mu ’ya’yan Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun.
Zamanai sukan zo zamanai su wuce,
amma duniya tana nan har abada.
Rana takan fito rana ta kuma fāɗi,
ta kuma gaggauta zuwa inda takan fito.
Iska takan hura zuwa kudu ta kuma juya zuwa arewa;
tă yi ta kewayewa, tă yi ta koma inda take fitowa.
Dukan rafuffuka sukan gangara zuwa teku,
duk da haka teku ba ya cika.
Daga inda rafuffukan suke fitowa,
a can suke komawa kuma.
Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.
Yesu Kiristi ba ya sākewa, shi ne a jiya, shi ne a yau, shi ne kuma har abada.
Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, "Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita."
Gama in, ta wurin laifin mutum ɗaya, mutuwa ta yi mulki ta wurin mutum ɗayan nan, ashe, waɗanda suka sami kyautar alherin Allah a yalwace da kuma kyautar adalci za su yi mulki a wannan rayuwa ta wurin mutum ɗayan nan, Yesu Kiristi.
Zai sa yaudara ta ƙara yin yawa, zai ɗaukaka kansa. Sa’ad da suke ji sun sami mafaka, zai hallaka mutane da yawa sa’an nan kuma yă fara gāba da Sarkin sarakuna. Duk da haka za a hallaka shi, amma ba da ikon mutum ba.