Pular para o conteúdo
Publicidade

Nascimento de Jesus

Por Bíblia Online

O nascimento de Jesus é o evento que divide a história. O Verbo se fez carne e habitou entre nós. Deus enviou seu Filho ao mundo para nos salvar e nos reconciliar consigo.

O Verbo se fez carne

Jesus não nasceu por acaso — sua encarnação foi planejada antes da fundação do mundo. Ele se esvaziou e assumiu a forma humana por amor.

A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.

Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake,

bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,

amma ya mai da kansa ba kome ba,

yana ɗaukan ainihin surar bawa,

aka yi shi cikin siffar mutum.

Aka kuma same shi a kamannin mutum,

ya ƙasƙantar da kansa

ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa,

mutuwar ma ta gicciye!

Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka, domin fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ya’ya.

Da yake ya’yan suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamanninsu na mutum domin ta wurin mutuwarsa hallaka wanda yake riƙe da ikon mutuwa, wato, Iblis ya kuma yantar da waɗanda dukan rayuwarsu tsoron mutuwa ya riƙe su cikin bauta.

Saboda wannan dole a mai da shi kamar yan’uwansa ta kowace hanya, domin zama babban firist mai aminci da mai jinƙai cikin hidima ga Allah, kuma miƙa hadayar sulhu saboda zunuban mutane.

Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada hallaka sai dai sami rai madawwami.

O anúncio e o nascimento

O nascimento de Jesus foi anunciado por anjos, precedido por sinais e recebido com adoração pelos pastores e pelos magos do oriente.

Haihuwar Yesu Kiristi

Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance. An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf. Amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar Maryamu tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki.

Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, "Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne. Za haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, yana ceto. gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu."

Duk wannan ya faru ne, don a cika abin da Ubangiji ya faɗi ta bakin annabin cewa, "Ga shi budurwa za yi ciki, za haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel" (wanda yake nufin "Allah tare da mu").

Da Yusuf ya farka daga barci, sai ya bi umarnin mala’ikan Ubangiji, ya ɗauki Maryamu zuwa gida a matsayin matarsa. Amma bai kwana da ita ba, sai bayan da ta haifi ɗan. Ya kuwa sa masa suna Yesu.

Amma mala’ikan ya ce mata, "Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah. Ga shi za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa, za ki kuma ba shi suna Yesu. Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar kakansa Dawuda, zai yi mulkin gidan Yaƙub har abada, mulkinsa kuma ba zai taɓa ƙare ba."

Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne. Ya tafi can don a rubuta shi tare da Maryamu, wadda aka yi masa alkawari zai aura, tana kuwa da ciki. Yayinda suke can, sai lokacin haihuwar jaririn ya yi, ta kuwa haifi ɗanta na fari. Ta nannaɗe shi a zane ta kuma kwantar da shi cikin wani kwami, don ba su sami ɗaki a masauƙi ba.

Amma mala’ikan ya ce musu, "Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane. Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji. Wannan zai zama alama a gare ku. Za ku tarar da jariri a nannaɗe a zane kwance a kwami."

Da mala’ikun suka bar su, su suka koma sama, sai makiyayan suka ce wa juna, "Mu je Betlehem mu ga wannan abin da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar mana."

Sai suka tafi da sauri, suka tarar da Maryamu da Yusuf, da kuma jaririn kwance a kwami. Sa’ad da suka gan shi, sai suka baza maganar da aka gaya musu game da yaron, duk kuwa waɗanda suka ji wannan, suka yi mamaki a kan abin da makiyayan suka faɗa.

O Rei que veio servir

Jesus nasceu para ser Rei, e todo aquele que é da verdade ouve a sua voz. Os magos o adoraram e ofereceram seus tesouros.

Sai Bilatus ya ce, "To, wato, kai sarki ne!"

Yesu ya amsa ya ce, "Haka yake, ni sarki ne yadda ka faɗa. Tabbatacce, saboda wannan dalili ne aka haife ni, kuma don wannan ne na zo duniya, domin in shaidi gaskiya. Duk wanda yake gefen gaskiya yakan saurare ni."

Bayan sun saurari sarki, sai suka kama hanyarsu, tauraron da suka gani a gabas kuwa yana tafe a gabansu, sai da ya kai inda yaron yake. Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki ƙwarai. Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur. Bayan an gargaɗe su cikin mafarki kada su koma wurin Hiridus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.

Seja o primeiro