Publicidade

Natal

Por Bíblia Online

O Natal celebra o maior milagre da história: Deus se fez homem. O menino Jesus, nascido em Belém, é Emanuel — Deus conosco — a esperança do mundo inteiro.

O nascimento do Salvador

O anjo anunciou: hoje vos nasceu um Salvador, que é Cristo, o Senhor! A virgem concebeu pelo Espírito Santo e deu à luz o Filho de Deus.

Amma mala’ikan ya ce musu, "Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane.

Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji.

Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne. Ya tafi can don a rubuta shi tare da Maryamu, wadda aka yi masa alkawari zai aura, tana kuwa da ciki.

Yayinda suke can, sai lokacin haihuwar jaririn ya yi, ta kuwa haifi ɗanta na fari. Ta nannaɗe shi a zane ta kuma kwantar da shi cikin wani kwami, don ba su sami ɗaki a masauƙi ba.

A profecia cumprida

Isaías profetizou: a virgem conceberá e dará à luz um filho que se chamará Emanuel. Em Jesus, essa promessa se cumpriu perfeitamente.

Saboda haka Ubangiji kansa zai ba ku alama. Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, za tă kuwa kira shi Immanuwel.

Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, "Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne.

Za tă haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, yana ceto. gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu."

Duk wannan ya faru ne, don a cika abin da Ubangiji ya faɗi ta bakin annabin cewa, "Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel" (wanda yake nufin "Allah tare da mu").

Glória a Deus nas alturas

Os pastores glorificaram a Deus e os anjos cantaram: 'Glória a Deus nas alturas e paz na terra entre os homens a quem Ele quer bem!'

"Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama,

a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu."

Makiyayan kuwa suka koma, suna ɗaukaka suna kuma yabon Allah saboda dukan abubuwan da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-22_10-02-25-