Pular para o conteúdo
Publicidade

Nova criatura

Por Bíblia Online

Em Cristo somos nova criação. O velho se foi, tudo se fez novo. A transformação não é reforma — é renascimento completo pelo poder do Espírito Santo.

Novas criaturas em Cristo

Se alguém está em Cristo, nova criação é. As coisas velhas passaram e eis que tudo se fez novo. A transformação é radical e total.

Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo!

Kaciya ko rashin kaciya ba wani abu ba ne; abin da yake da amfani shi ne sabuwar halitta.

Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.

Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. "Ina yin kome sabo!" Sai ya ce, "Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma."

Despir o velho e vestir o novo

Somos chamados a despir o velho homem e vestir o novo, criado segundo Deus em justiça e santidade provenientes da verdade.

sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta , wadda take lalacewa saboda sha’awace-shaawacen da suke ruɗe ku. A maimakon haka, bari Ruhu sabunta tunaninku da kuma halayenku. Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, bayyana cikin adalci, da zaman tsarki.

Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa.

Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka da Kiristi daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa.

In kuwa mun zama ɗaya tare da shi haka a cikin mutuwarsa, tabbatacce mu ma za mu zama ɗaya tare da shi cikin tashinsa daga matattu. Gama mun san cewa an gicciye halayenmu na tare da shi domin a kawar da jikin nan mai zunubi don kada mu ƙara zama bayi ga zunubi domin duk wanda ya mutu an yantar da shi daga zunubi ke nan.

An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.

Coração e Espírito novos

Deus promete dar um coração novo e um espírito novo. Pelo novo nascimento somos feitos participantes da natureza divina.

Zan ba su zuciya ɗaya in kuma sa sabon ruhu a cikinsu; zan fid da zuciyar dutse daga gare su in kuma ba su zuciya ta nama. Sa’an nan za su bi ƙa’idodina su kuma yi hankali ga kiyaye dokokina. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu.

Yesu ya amsa ya ce, "Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa."

Ta wurin waɗannan ya ba mu alkawaransa masu girma da kuma masu daraja, domin ta wurinsu ku iya yin tarayya cikin Allahntakarsa, ku kuma kuɓuta daga lalatar da take cikin duniya wadda mugayen sha’awace-shaawace suke jawowa.

"Ku manta da abubuwan da suka riga suka faru;

kada ku yi tunanin abin da ya riga ya wuce.

Duba, ina yi abu sabo!

Yanzu yana faruwa; ba ku gan shi ba?

Ina yin hanya a cikin hamada

rafuffuka kuma a cikin ƙeƙasasshiyar ƙasa.

Seja o primeiro