Pular para o conteúdo
Publicidade

Ouvir a voz de Deus

Por Bíblia Online

Ouvir a voz de Deus é o privilégio supremo do cristão. Ele fala por sua Palavra, pelo Espírito e em circunstâncias — e as ovelhas reconhecem a voz do bom Pastor.

As ovelhas ouvem a voz do Pastor

Jesus disse: minhas ovelhas ouvem minha voz, eu as conheço e elas me seguem. A relação com Deus é íntima e pessoal.

Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na.

A rubuce yake a cikin Annabawa cewa, Allah zai koyar da dukansu. Duk wanda ya saurari Uba, ya kuma koyi daga wurinsa, zai zo wurina.

Wanda yake na Allah, yakan ji abin da Allah yake faɗi. Abin da ya sa ba kwa jin sa kuwa shi ne don ku ba na Allah ba ne."

"Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai. Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu.

Kalman ya zama mutum

Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne.

Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.

Deus fala pela Palavra

Toda Escritura é inspirada por Deus. A Bíblia é a voz confiável de Deus registrada para nos guiar em toda verdade.

Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci, domin mutumin Allah zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.

Gaba da kome dai, dole ku gane cewa babu annabcin Nassin da ya fito daga fassarar annabi da kansa. Gama annabci bai taɓa samo tushensa daga nufin mutum ba, sai dai mutane sun yi magana daga Allah yayinda Ruhu Mai Tsarki ya bishe su.

Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi.

Magini mai hikima da marar hikima

"Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse. Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse.

Yesu ya amsa ya ce, "A maimakon, masu albarka ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma biyayya da ita."

Buscar e ouvir

Deus promete: 'Clama a mim, e te responderei.' Quando buscamos sinceramente sua voz, encontramos direção e revelação.

Kira gare ni zan kuwa amsa maka in kuma faɗa maka manyan abubuwan da ba a iya kaiwa, da ba ka sani ba.

Ko kun juye dama ko hagu, kunnuwanku za su ji murya a bayanku tana cewa, "Ga hanya; ku yi tafiya a kai."

Kuka kuma ce, "Ubangiji Allahnmu ya nuna mana ɗaukakarsa da zatinsa, mun kuma ji muryarsa a tsakiyar wutar. A yau mun ga cewa mutum zai iya rayu idan ma Allah ya yi magana da shi.

Muryar Ubangiji tana a bisa ruwaye;

Allah Maɗaukaki ya yi tsawa,

Ubangiji ya yi tsawa a bisa manyan ruwaye.

Muryar Ubangiji mai iko ce;

muryar Ubangiji da girma take.

Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon.

Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu.

Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi,

ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela

Seja o primeiro