Publicidade

Ouvir

Por Bíblia Online

Ouvir é uma disciplina espiritual essencial. A Bíblia exorta: 'Quem tem ouvidos, ouça.' A fé vem pelo ouvir, e ouvir é mais que escutar — é obedecer e agir.

A fé vem pelo ouvir

Sem ouvir a Palavra, não há fé. A pregação do evangelho gera fé nos corações de quem ouve com disposição e humildade.

Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi.

Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi.

To, ta yaya za su kira ga wanda ba su gaskata ba? Ta yaya kuma za su gaskata wanda ba su taɓa ji ba? Ta yaya kuma za su ji ba tare da wani ya yi musu wa’azi ba?

Duk mai kunnen ji, ji."

A kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa,

" Za ku yi ta ji amma ba za ku taɓa ganewa ba;

za ku yi ta kallo amma ba za ku taɓa gani ba.

Gama zuciyar mutanen nan ta taurare;

da ƙyar suke ji da kunnuwansu,

sun kuma rufe idanunsu.

Da ba haka ba, mai yiwuwa su gani da idanunsu,

su kuma ji da kunnuwansu,

su gane a zuciyarsu,

su kuwa juya, in kuma warkar da su.

Ouvir e obedecer

Não basta ouvir — é preciso praticar. Quem ouve a Palavra e a pratica é como o homem sábio que edificou sobre a rocha.

Kada ku zama masu ji kawai, ku ruɗi kanku. A maimakon haka ku zama masu yin abin da ta ce.

Kada ku zama masu ji kawai, ku ruɗi kanku. A maimakon haka ku zama masu yin abin da ta ce.

Saurarawa da kuma aikatawa

Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba,

Saurarawa da kuma aikatawa

Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba, gama fushin mutum ba ya kawo rayuwar adalcin da Allah yake so.

Magini mai hikima da marar hikima

"Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse.

Magini mai hikima da marar hikima

"Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse. Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse. Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi. Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa."

Yesu ya amsa ya ce, "A rubuce yake cewa, Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah."

Yesu ya amsa ya ce, "A maimakon, masu albarka ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma biyayya da ita."

Yesu ya amsa ya ce, "A maimakon, masu albarka ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma biyayya da ita."

Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.

Deus ouve nossas orações

O Senhor ouve os que clamam a Ele de coração sincero. Ele inclina os ouvidos para as nossas súplicas e responde com fidelidade.

Ina ƙaunar Ubangiji, gama ya ji muryata;

ya ji kukata ta neman jinƙai.

Domin ya juye kunnensa gare ni,

zan kira gare shi muddin ina da rai.

Cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji;

Na yi kuka ga Allahna don taimako.

A Haikalinsa ya ji muryata,

Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.

Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci

kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;

Da safe, ya Ubangiji, ka ji muryata;

da safe na gabatar da bukatuna a gabanka

in kuma jira da sa zuciya.

Bari in ji farin ciki da murna;

bari ƙasusuwan da ka ragargaza su yi farin ciki.

Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa,

gama na sa zuciyata a gare ka.

Ka nuna mini hanyar da zan bi,

gama a gare ka na miƙa raina.

Wannan shi ne ƙarfin halin da muke da shi sa’ad da muke zuwa a gaban Allah, gama mun san cewa kome muka roƙa bisa ga nufinsa, yakan saurare mu.

In kuwa muka san cewa yana sauraranmu, ko mene ne muka roƙa, mun sani, mun riga mun sami abin da muka roƙa daga gare shi ke nan.

Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku.

Kira gare ni zan kuwa amsa maka in kuma faɗa maka manyan abubuwan da ba a iya kaiwa, da ba ka sani ba.

Zunubi, furci da kuma fansa

Tabbatacce hannun Ubangiji bai kāsa yin ceto ba,

kunnensa kuma bai kurmance da zai kāsa ji ba.

Ouvir a voz de Deus

Jesus disse: 'As minhas ovelhas ouvem a minha voz.' Deus fala através da Palavra, do Espírito e das circunstâncias — cabe a nós ouvir.

Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na.

"Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai. Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu.

Ga ni! Ina tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa. Duk wanda ya ji muryata ya kuma buɗe ƙofar, zan shiga in kuma ci tare da shi, shi kuma tare da ni.

Ga ni! Ina tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa. Duk wanda ya ji muryata ya kuma buɗe ƙofar, zan shiga in kuma ci tare da shi, shi kuma tare da ni.

Ubangiji Allahnku ne za ku bi, shi ne kuma za ku girmama. Ku kiyaye umarnansa, ku kuma yi masa biyayya; ku bauta masa, ku kuma manne masa.

Allah ya ba ku Ruhunsa yana kuma aikata ayyukan banmamaki a cikinku saboda kuna kiyaye Doka ne, ko kuwa domin kuna gaskatawa abin da kuka ji ne?

Sabedoria no ouvir

Seja pronto para ouvir e tardio para falar. A sabedoria começa com a disposição de ouvir instrução e aceitar correção.

Duk wanda yakan ba da amsa kafin ya saurara,

wannan wauta ce da kuma abin kunya.

Duk wanda ya mai da hankali ga umarni yakan yi nasara,

kuma mai albarka ne wanda yake dogara ga Ubangiji.

Gargaɗi a kan zina

Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka

kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

Duk wanda ya mai da hankali ga horo kan nuna hanyar rai,

amma duk wanda ya ƙyale gyara kan sa waɗansu su kauce.

In wani ya yi kunnuwa ƙashi ga doka

ko addu’arsa ma abar ƙyama ce.

Gara ka saurari tsawatawar mai hikima

da ka saurari waƙar wawaye.

Dukan abubuwa suna kawo gajiya,

gaban magana.

Ido ba ya gaji da gani,

haka ma kunne ƙoshi da ji.

" In kuka ci gaba da tayar mini, kuka ƙi ku saurare ni, zan ninka wahalolinku sau bakwai, yadda ya dace da zunubanku.

In ba ku saurara ba, in kuma ba ku sa zuciyarku ga girmama sunana ba, zan aukar muku da la’ana, zan kuma la’antar da albarkunku. I, na riga na la’anta su, domin ba ku sa zuciyarku ga girmama ni ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.

Amma sa’ad da na yi maka magana, zan buɗe bakinka za ka kuwa faɗa musu cewa, Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.Duk mai ji ya ji, kuma duk wanda ya ƙi ji, ya ƙi ji; gama su gida ne na yan tawaye.

"Ranakun suna zuwa," in ji Ubangiji Mai Iko Duka,

"sa’ad da zan aika da yunwa cikin ƙasar,

ba yunwar abinci ko ta ƙishirwa ba,

sai dai yunwa ta jin maganar Ubangiji.

Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran yan kurkuku kuwa suna sauraronsu.

Yoshuwa ya ce wa Isra’ilawa, "Ku zo nan ku ji maganar Ubangiji Allahnku.

Abin da kuka faɗa a cikin duhu, za a ji shi a hasken rana. Kuma abin da kuka faɗa a kunne, a cikin ɗakunan ciki-ciki, za a yi shelarsa daga kan rufin ɗakuna.

Ɗan’uwa da ya yi maka laifi

"In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan.

Ɗan’uwa da ya yi maka laifi

"In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan. Amma in bai saurare ka ba, ka je tare da mutum ɗaya ko biyu, domin a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku. In kuwa ya ƙi saurare su, sai ka gaya wa ikkilisiya; in kuma ya ƙi saurari ikkilisiya ma, ka yi da shi kamar marar sanin Allah ko mai karɓar haraji.

Yetro ya yi murna da jin duk abubuwa masu kyau da Ubangiji ya yi wa Isra’ila, wajen cetonsu daga hannun Masarawa.

Raƙumar ruwan mutuwa sun kewaye ni;

raƙumar ruwan hallaka suna cin ƙarfina.

Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe ni;

tarkuna kuma suka auka mini.

"A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji;

na yi kira ga Allahna.

Daga cikin haikalinsa ya saurare muryata;

kukata ta zo kunnensa.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-