Publicidade

Amós 8

Kwandon nunannun ya’yan itace

1 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji ya nuna mini kwandon nunannun ya’yan itace. 2 Ya yi tambaya ya ce, "Me ka gani Amos?"

Sai na amsa na ce, "Kwandon nunannun ya’yan itace."

Sai Ubangiji ya ce mini, "Lokaci ya yi wa mutanena Isra’ila da ba zan ƙara barinsu ba.

3 "A ranan nan," in ji Ubangiji Mai Iko Duka, "Waƙoƙin a haikali za su koma makoki.8.3 Ko kuwa "mawaƙar haikali za su yi makoki" Za a ga gawawwaki a ko’ina! Shiru!"

4 Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata

kuka kori matalautan ƙasar.

5 Kuna cewa,

"Yaushe Sabon Wata zai wuce

don mu sayar da hatsi,

Asabbaci ta wuce,

don mu sayar da alkama?"

Mu yi awo da ma’aunin zalunci

mu ƙara kuɗin kaya

mu kuma cutar da mai saya,

6 mu sayi matalauta da azurfa

masu bukata kuma da takalmi,

mu sayar da alkamar haɗe da yayi.

7 Ubangiji ya rantse da Girman Yaƙub, "Ba zan taɓa mantawa da duk wani abin da suka yi ba.

8 "Shin, ƙasar ba za yi rawan jiki saboda wannan ba,

kuma duk masu zama a cikinta ba za su yi makoki ba?

Ƙasar duka za hau ta sauka kamar Nilu;

za a dama ta sa’an nan ta nutse

kamar kogin Masar.

9 "A wannan rana," in ji Ubangiji Mai Iko Duka,

"Zan sa rana ta fāɗi da tsakar rana

in kuma duhunta duniya da rana tsaka.

10 Zan mai da bukukkuwanku na addini su zama makoki

kuma dukan waƙoƙinku su zama kuka.

Zan sa dukanku ku sa rigunan makoki

za ku kuma aske kawunanku.

Zan sa wannan lokaci zama kamar lokacin da ake makokin ɗan tilon da ake da shi

kuma ƙarshenta kamar rana mai ɗaci.

11 "Ranakun suna zuwa," in ji Ubangiji Mai Iko Duka,

"sa’ad da zan aika da yunwa cikin ƙasar,

ba yunwar abinci ko ta ƙishirwa ba,

sai dai yunwa ta jin maganar Ubangiji.

12 Mutane za su yi ta tangaɗi daga teku zuwa teku

suna yawo daga arewa zuwa kudu,

suna neman maganar Ubangiji,

amma ba za su samu ba.

13 "A wannan rana

"kyawawan yan mata da kuma samari masu ji da ƙarfi

za su suma don ƙishirwa.

14 Waɗanda suka yi rantsuwa da abin kunya8.14 Ko kuwa da Ashima; ko da gunki na Samariya,

ko kuma su ce, Muddin allahnku yana a raye, ya Dan,

ko kuwa, Muddin allahn8.14 Ko kuwa iko Beyersheba yana a raye,

za su fāɗi,

ba kuwa za su ƙara tashi ba."

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-