Pular para o conteúdo
Publicidade

O papel da mulher

Por Bíblia Online

A Bíblia honra a mulher como colaboradora essencial no plano de Deus. De Provérbios 31 às mulheres do Novo Testamento, a Escritura celebra a sabedoria, a força e a fé feminina.

A mulher virtuosa

Mulher virtuosa, quem a achará? Seu valor excede o de rubis. Ela é sábia, trabalhadora, generosa e temida pelo Senhor.

Wa yake iya samun mace mai halin kirki?

Darajarta ta fi ta lu’uluai.

Mijinta yana da cikakken amincewa da ita

kuma ba ya rasa wani abu mai daraja.

Takan yi masa alheri ba mugunta ba,

dukan kwanakin ranta.

Takan zaɓi ulu da lilin

ta yi ta saƙa da hannuwanta da farin ciki.

Ita kamar jirgin yan kasuwa ne

tana kawo abincinta daga nesa.

Takan farka tun da sauran duhu;

ta tanada wa iyalinta abinci

ta kuma shirya wa yan matan gidanta ayyukan da za su yi.

Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta;

daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi.

Takan himmantu yi aikinta tuƙuru;

hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta.

Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta,

kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare.

Da hannunta take riƙe abin kaɗi

ta kuma kama abin saƙa da yatsotsinta.

Takan marabci talakawa

takan kuma taimaki masu bukata.

Takan yi riguna na lilin ta sayar;

takan kuma sayar wa yan kasuwa da ɗamara.

Ƙarfi da mutunci su ne suturarta;

za iya yin dariyar kwanaki masu zuwa.

Tana magana da hikima,

kuma umarnai mai aminci yana a harshenta.

Tana lura da sha’anin gidanta

kuma ba ta cin abincin ƙyuya.

Mace mai hikima kan gina gidanta,

amma da hannunta wawiya takan rushe shi ƙasa.

Jan kunne game da jaraba

Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka

kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.

Beleza interior

A beleza verdadeira não é exterior, mas o caráter incorruptível de um espírito manso e tranquilo. Isso tem grande valor diante de Deus.

Matan aure da mazan Aure

Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba sa’ad da suka ga rayuwarku mai tsabta da kuma na ladabi. Kyanku bai kamata zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada. Maimakon haka, kyanku ya kamata zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah. Gama haka matan masu tsarki na waɗanda suka sa begensu ga Allah suka yi wa kansu ado. Sun yi wa mazansu biyayya, kamar Saratu, wadda ta yi biyayya ga Ibrahim, har ta kira shi maigidanta. Ku ya’yanta ne mata in kun aikata abin da yake daidai, ba ku kuma ba tsoro dama ba.

Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu hana addu’oinku.

Ina kuma so mata su lura su yi wa kansu adon da ya cancanta, da rigunan da suka dace, ba da adon kitso ko sa kayan zinariya ko lu’uluu ko kuma tufafi masu tsada ba,

A haka kuma, dole matansu su zama matan da suka cancanci girmamawa, ba masu gulma ba, sai dai masu sauƙinkai da kuma masu aminci a cikin kome.

Parceria e dignidade

Deus criou homem e mulher à sua imagem. A mulher não é inferior, mas parceira e co-herdeira da graça da vida.

Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.

Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.

Miji da mace ya halicce su.

Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, "Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa."

Ubangiji Allah ya ce, "Bai yi kyau mutumin kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi."

Sa’an nan ya ce wa macen,

"Zan tsananta naƙudarki ainun,

da azaba kuma za ki haifi ya’ya.

Za ki riƙa yin marmarin mijinki

zai kuwa yi mulki a kanki."

Duk da haka a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, namiji kuma ba a rabe yake da mace ba. Kamar yadda mace ta fito daga namiji, haka kuma aka haifi namiji ta wurin mace. Sai dai kowane abu daga Allah yake.

Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji ne kuke yi. Gama miji shi ne kan mace, yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa. To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome.

Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari. Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ya’yansu, su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani rena maganar Allah.

Seja o primeiro